Tarihin Shugaba Mugabe na Zimbabwe; Duk abin da kuke buƙatar sani

A duk lokutan da aka shafe inda tattalin arzikin Zimbabwe ya yi ta tabarbarewa tsawon shekaru, an sha hasashen durkushewar Robert Mugabe ta fuskar siyasa da ma ta lafiya, sai dai ya tsallake wannan fata, har sai yanzu da wani abu ya faru.
Haka kuma, ana ganin kamar ya wuce gona da iri wajen ganin cewa matarsa ta gaje shi, hakan ne kuma ta sa shugabannin soji wadanda da bazarsu yake rawa a mulkin, suka daina ba shi goyon baya.
Halin lafiyarsa dai ya ci gaba da tabarbarewa cikin shekarun da suka gabata, kasancewar sa dan shekara 93, duk da cewa a hukumance ya yi aniyar sake tsayawa takara.
Kafin zaben shekarar 2008, ya ce: "Idan ka fadi zabe kuma mutane suka juya maka baya, to lokacin barin siyasa ya yi."
Amma bayan da Morgan Tsvangirai ya yi nasara a kansa, sai Mista Mugabe ya fiddo wasu halaye da suka saba da maganar tasa, inda ya yi rantsuwa cewa 'Allah ne kadai' zai iya tsige shi daga ofis.
Amma don ya tabbatar da ikon nasa, sai ya dinga amfani da rikici.
Shi kuwa Mista Tsvangirai a kokarinsa na kare magoya bayansa, sai ya janye daga zagaye na biyu, amma duk da haka an tilasta Mista Mugabe ya sanya Mista Tsvangirai a matsayin mataimakinsa, shi kuma ya ci gaba da mulkin da ya fara tun shekarar 1980.
Babban abun da ya sa Mista Mugabe ya yi suna shi ne yakin da aka yi a shekarun 1970.
Tarihin rayuwar Robert Mugabe
 Image caption Shugaba Mugabe ya bai wa matarsa Grace goyon bayan zama mataimakiyar shugaba

Jigo a juyin-juya hali

Akwai lokacin da ake yi masa kallon wani jigo a juyin-juya hali, inda yake fada da tsirarun Turawa don neman 'yancin al'ummarsa - wannan ne dalilin da ya sa shugabannin Afirka da dama suke sako-sako wajen sukar sa.
Tun bayan da Zimbabwe ta samu 'yancin kai, an samu ci gaba a duniya, amma shi har yanzu tunaninsa na zamanin da ne.
 Image caption Ana iya ganin Robert Mugabe nan (a hagu), cikin 1960, inda ya samu kaimi daga akidojin naka-sai-naka a Afirka
Har yanzu jaruman yakin kwato yanci na jam'iyyar Zanu-PF na yakar munanan akidun jari hujja da mulkin mallaka.
A kan yi watsi da masu suka ana kwatanta su da maciya amana, abin da ke tunowa da yakin sari-ka-noke, lokacin da alakanta mutum da wannan kalmar tamkar hukuncin kisa ne.
Ya sha dora alhakin matsin tattalin arzikin da Zimbabwe ke fama da shi a kan kasashen yamma, karkashin jagorancin Birtaniya, don hambarar da shi saboda kwace gonakin Turawa da ya yi.
Masu sukarsa na yawan zargin sa da cewa ba ya nuna damuwa kan yadda tattalin arzikin zamani ke aiki.
Ya fi mayar da hankali kan tambayar yadda za a raba zarikin kasa, maimakon neman hanyar da za a inganta shi.
 Image caption Masu zanga-zanga a shekarar 2016 sun kona kudin kasar da ba shi da daraja don nuna kin amincewa da gabatar da takardun lamuni a matsayin kudi
Mr Mugabe ya taba cewa tattalin arzikin kasar da zai taba durkushewa gaba daya ba, kasancewar kasarsa ta fuskanci matsalar tattalin arziki mafi kamari a duniya, da kuma hauhuawar farashi da ya taba kai wa kashi miliyan 231 a watan Yulin 2008, kai ka ce yana so ne ya gwada ikirarin nasa.
Farfesa Tony Hawkins na jami'ar Zimbabwe ya taba fuskantar wani abu tattare da shugaban Zimbabwe, inda ya ce: "A duk lokacin da batun tattalin arziki ya hadu da siyasa, to siyasa ce ke yin nasara."
A shekarar 2000, ya fuskanci kakkarfar hamayya a karon farko, ya damalmala tattalin arzikin kasar don samun karfin iko a siyance.
Ya kwace gonakin Turawa wadanda su ne kashin bayan tattalin azrikin kasar, ya kuma fatattaki kungiyoyin tallafi, wato dai cikin siyasa Mista Mugabe ya yi wa makiyansa shigar-burtu - ya ci gaba da kasancew a mulki.

Ko ta halin kaka

Kuma dabarun da shi da magoya bayansa suka yi amfani da su, sun samo su ne daga yakin sari-ka-noken da aka yi a can baya.
Bayan da ya sha kaye a karon farko a zaben raba gardamar shekarar 2000, Mista Mugabe ya kaddamar da mayakan sa kai na kashin kansa, wasu tsofaffin sojoji 'yan mazan jiya, da dakarun tsaro ke marawa baya - wadanda ke amfani da rikici da kashe-kashe a matsayin matakan zabe.
 Image caption Mista Mugabe na cewa yana gwagwarmaya ne don kwatar 'yancin bakaken fata 'yan Zimbabwe
Bayan shekara takwas, an sake bin irin wannan salon bayan da Mista Mugabe ya fadi a zagayen farko na zaben shugaban kasa.
A duk lokacin da aka bukata, a kan yi amfani da dakarun tsaro da kafafen yada labarai na gwamnati, wadanda mambobin jam'iyyar Zanu-PF ne, wajen yi wa jam'iyya mai mulki hidima.
Mutumin wanda ya yi gwagwarmaya kan mutum-daya, kuri'a-daya ya bullo da wani sharadi na cewa mutanen da suka cancanci zabe sai sun tabbatar sun 'yan kasa ne ta hanyar gabatar da takardun shaida na biyan kudin lantarki ko ruwan famfo, abin da kyar ne matasa da tsantsar masu zabe marasa aikin yi 'yan adawa, idan suna da su.
Daya daga cikin nasarorin da tsohon malamin da ya shafe tsawon shekara 33 a kan mulki, ba ko tantama ya iya cimmawa ita ce fadada ilmi.
Zimbabwe a baya-bayan nan na da alkaluman mutanen da suka iya karatu da rubutu mai yawa a Afirka da kashi 90% na al'ummarta.
Masanin kimiyyar siyasa a yanzu marigayi Masipula Sithole ya taba cewa bunkasa ilmin da shugaban kasar ke yi tamkar "hakawa kansa kabari" ne.
Matasan da suka ci gajiyar haka na iya yin tankade da rairaya kan matsalolin Zimbabwe da kansu kuma akasari suna zargin cin hanci da rashin iya gudanarwar da suka dabaibaye gwamnati a matsayin silar rashin samun ayyuka da kuma hauhawar farashi.

Mai riƙon ƙaho

Mista Mugabe na iya yin imani cewa abu ne mai sauki a mulki kasar manoma masu neman abin da za su kai cikinsu da saurin mika wuya a kan zaratan matasa masu karfi a jika da suka koshi da ilmi.
Ya yi ikirarin yana gwagwarma ne don talakawan karkara sai dai filaye da dama da ya kwace sun koma hannuwan 'yan barandansa.
 
Mugabe bai taba tsoron yin amfani da tarzoma ba don ci gaba da mulki
Babban limamin kiristan nan, Desmond Tutu ya taba cewa dadadden shugaban na Zimbabwe ya zama kwatankwacin 'yan kama-karyan Afirka masu riƙon ƙaho.
A lokacin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na 2002, ya fara sanya riguna masu launukan sheki da ke dallare fuskarsa - wani salo na shugabannin Afirka masu mulkin danniya.
A cikin shekaru ashirin dinsa na farko, ana ganin dan ra'ayin riƙwan ne kawai a bainar jama'a cikin shigar jaket da lakatayel ko kuma hartin da wando.
An bar 'yan Zimbabwe da yawa, har ma da wasu na tambayar me ya sa ba zai sawwake wa kansa ya je ya huta a 'yan shekarun da suka rage masa da matashiyar matarsa ba.
Matarsa ta biyu, Grace, wadda ya ba wa ratar shekara 40, ta taba cewa yakan tashi da karfe hudun dare ya kama motsa jikin da ya saba kullum.
Mista Mugabe yana dan shekara 73 lokacin da ta haifa musu dansu na uku, Chatunga.
Yana da'awar shi riƙaƙƙen dan katolika ne, kuma lokaci-lokaci jami'an tsaro kan mamaye masu ibada a Majami'ar Katolika ta Harare duk ranar Lahadin da ya je addu'a.
Sai dai, imanin Mugabe bai hana shi samun 'ya'ya guda biyu da Grace ba, lokacin da take sakatariyarsa, yayin da fitacciyar uwargidansa mutuniyar Ghana, Sally, ke fama da jinyar ajali sakamakon cutar kansa.
'Sarki'
Ko da yake, Robert Mugabe ya yi wa mutuwar da ake ta kira masa ƙwari, sai dai shekarun da suka laftu a kansa sun fara yi masa nauyi a baya-bayan nan, inda kaifin bakin da aka san shi da shi a baya, yanzu kan koma cike da gajiya idan yana jawabi.
Wani sakon diflomasiyya na Amurka a shekara ta 2011, da shafin kwarmata bayanai na Wkileaks ya fitar na nuna cewa Mugabe na fama da cutar daji.
 Image caption Matarsa Grace ta ce Mista Mugabe kan farka tsakar dare don motsa jininsa
Idan ba wannan ba, a ko da yaushe Mista Mugabe ya kasance mutum mai tsananin alfahari.
Sau da dama yana cewa zai sauka daga mulki ne kawai idan kammala cika burinsa na "juyin juya hali".
Wannan na nufin sake raba gonakin fararen fata, yana kuma so ya zabi mutumin da zai gaje shi da hannunsa, wanda tabbas zai fito daga cikin jam'iyyarsa ta Zanu-PF.
Didymus Mutasa, da ya taba zama makusantan Mista Mugabe amma yanzu sun yi hannun riga, ya taba fada wa BBC cewa a al'adar Zimbabwe, ana maye gurbin sarakuna ne kadai idan sun mutu "kuma Mugabe sarkinmu ne".
Sai dai ga alama kamar wasu daga cikin tsoffin abokan tafiyarsa ba su shirya wa kafuwar daular ba.

Labels: ,