An haifi Alhaji Shehu Shagari a
kauyen Shagari a shekarar 1925, kuma shi ne da na shida ga mahaifinsa
Aliyu, magajin kauyen Shagari, wanda manomi ne, dan kasuwa yana kuma
kiwo.
Allah ya yi wa mahifinsa rasuwa yana dan shekara biyar da haihuwa.
Alhaji
Shehu Shagari ya fara karatun kur'ani tun yana dan shekara hudu, kuma
daga bisani ya je makarantar Elimentari da ke garin Yabo kusa da kauyen
Shagari, daga nan kuma ya tafi makarantar Middle a Sokoto, daga nan kuma
ya je kwaleji ta Kaduna.
Bayan da ya kammala karatun
sakandirensa, Alhaji Shehu Shagari ya yi koyarwa a makarantun middle
daban-daban a matsayin malamin kimiyya da ma tarihi.
Tun yana
kwaleji, Shagari ya fara nuna sha'awar shiga siyasa, inda a shekarar
1946 shi da Malam Gambo Abuja suka kafa wata kungiyar matasa a Sokoto,
kuma sun samu goyan bayan dattijai kamar Sir Ahmadu Bello da Ibrahim
Gusau da kuma Malam Ahmadu Dabbaba.
A shekarar 1948 ne kuma aka
amince da a hade dukkanin kungiyoyin siyasar yankin zuwa kungiyar NPC
wadda daga bisani ta zama jam'iyyar da ta tsaya takara a zaben shekarar
1959.
Kafin wannan shekarar ne aka zabi Shagari a matsayin wakilin
mazabar Kudu-maso Kudancin Sokoto, kuma a shekarar 1958, an zabe shi a
matsayin sakataren majalisar Firaminista, Sir Abubakar Tafawa Balewa.
Daga
bisani Shagari ya rike mukaman minista daban-daban da suka hada da na
ci gaban tattalin arziki (1960), da na kula da harkokin cikin gida
(1962) da kuma na ayyuka da safiyo (1965).
Bayan juyin mulkin farko da sojoji suka yi, Alhaji Shehu Shagari ya koma gida Sokoto.
Da hawan janar Gowon ya bai wa Shagari ministan kula da harkokin tattalin arziki, daga bisani kuma aka ba shi ministan kudi.
Shehu Shagari yazama shugaban kasar Nijeriya a watan Oktoban shekarar
1979, yayi mulki har zuwa Disamban shekarar 1983, wanda soji suka kwace
mulki a hunnunsa, a jogorancin Muhammadu Buhari. Shagari shine shugaban
Nijeriya da yahau mulki ta sanadiyar zabe na farko. Olusegun Obasanjo
ne ya bayar da mulkin zuwa ga farin kaya, a dalilin suka da matsi da
mulkin sojojin ke fuskanta, ga rashin yin katabus, ganin hakan ne dai
yasa Obasanjon ya bayar da mulkin amma ba'a kai koina ba sai sojojin
suka sake dawowa suka kwace mulki daga Shagarin, inda suka zargi
mulkinsa da cin hanci da rashawa, hakane ne dai yakaiga Muhammadu Buhari ga zama shugaban kasar a wancan lokaci.