Tarihin mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo

Farfesa Yemi Osinbajo mutum ne da za a iya cewa dan-baiwa ne ganin irin nasarorin da ya samu a rayuwarsa tun daga yarinta har girmansa.
Ba ya ga karatun boko da ya yi mai zurfi, ya kuma yi nisa a harkar addinin Kirista, inda ya zamo limami a daya daga cikin manyan-manyan Majami'un Najeriya, kafin daga bisani kuma ya zamo mataimakin shugaban kasa.
Irin wannan nasarori da ya cimma ne suka sa wasu ke ganin zai iya gadar Shugaba Muhammadu Buhari idan ya kammala wa'adinsa a 2023.
An haifi Yemi Osinbajo ne a birnin Lagos a ranar 8 ga watan Maris na 1957. Ya yi karatun makarantun Firamare da sakandare a babban birnin kasuwancin na Najeriya.
Kuma tun a wannan mataki hazakarsa ta fara fitowa fili, inda ya lashe kyautuka da dama. Daga nan ne kuma ya tafi Jami'ar Legas, inda ya yi digiri na farko a fannin shari'a.
Daga nan kuma ya je fitacciyar jami'ar nan ta London wato School of Economics and Political Science, inda ya yi digiri na biyu a fannin na shari'ar.
Yemi Osinbajo ya yi aiki a kamfanoni daban-daban masu zaman kansu da na gwamnati. Ya rike kwamishinan shari'a na jihar Legas daga shekarar 1999 zuwa 2007.
Ya yi aiki a matsayin jami'in kwamitin kwararu na ladabtarwa da gyara halayyar dan Adam na majalisar dinkin duniya kan wanzar da zaman lafiya a fadin duniya.
Kazalika Farfesa ne a fannin shari'a a tsangayar koyar da aikin shari'a ta jami'ar Legas, kuma ya zama mai bayar da shawara na musamman ga babban mai shari'a na Najeriya a 1988-1992.
Ya yi aiki da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, sannan ya zama babban lauya na Najeriya wato SAN a 2002, ya kuma rike jami'in tuntuba na Majalisar Dinkin Duniya kan tattalin arzikin nahiyar Afrika.
Sannan ya zama wakilin kungiyar lauyoyi ta duniya zuwa Afrika ta kudu don tabbatar da cin gashin kan bangaren shari'a da kuma doka da oda.
Farfesa Osinbajo ya wallafa makaloli da dama a bangaren shari'a, da suka shafi 'yancin dan Adam musamman kan mata da kananan yara, tattalin arziki da abin da ya shafi cin hanci da rashawa.
Ya yi rubutu kan sauya dokokin bayar da shaida kan manyan laifuka a Najeriya da dai wasu da dama.

Osinbajo ya samu kyatuka da yawa a rayuwarsa tun daga mataki na makaranta har zuwa na aiki.
Ya lashe kyautar Graham Douglas a jami'ar Legas a shekarar 1975, ya samu kyautar kwarewa da nuna bajinta kan aiki daga kungiyar lauyoyi ta Najeriya. Ya kuma samu kyautar jaridar The Nation a matsayin mai shari'a na shekarar 2006.
Yemi Osinbajo yana da mata daya mai suna Dolapo Osinbajo da 'ya'yansu uku - namiji daya Fiyinfoluwa da kuma mata biyu Kiki da Kayinsola.
A shekarar 2015 ne Shugaban Najeriya mai-ci Muhammadu Buhari ya zabe shi a matsayin abokin takararsa na shugabancin kasar, suka kuma samu nasarar lashe zaben inda ya zama mataimakin shugaban kasa.
Sai kuma a 2019 da aka sake zabar su domin ci gaba da jan ragamar kasar a karo na biyu.

Labels: ,