Ranar 29 ga Oktoba jirgin sama kirar Boeing 737 Max, mallakar
kamfanin sufurin jiragen sama na Lion Air ya yi hadari da shi a tekun
Java jim kadan bayan tashinsa daga birnin Jakarta na kasar Indonesiya.
Daukacin fasinjoji 189 da matukan jirgin duk sun mutu, kuma wani mai aikin ceton sa-kai da ke iyo a ruwa shi ma ya halaka.
Masu
bincike sun ce (jirgin) na da matsala a cikin injinsa, wanda kamata ya
yi a dakatar da tashinsa (hada-hadar sufurinsa har sai an shawo kan
matsalarsa). 18 ga Mayu: Jirgi
kirar Boeing 737 mai daukar fasinjoji ya yi hadari, inda ya rikito jim
kadam da dagawarsa daga baban filin tashin jiragen sama na Jose Marti da
ke Havana (kasar Cuba), inda ya halaka mutane 112. 11 ga Afirilu: Jirgin
sama ya yi hadari jim kadan da dagawarsa sama a kusa da babban birnin
Aljeriya na Aljiers, wanda ya halaka daukacin fasinjoji 257, wadanda
suka hada da matukansa 10. Mafi yawan wadanda suka mutu sojoji ne da
iyalnsu. 12 ga Maris: Wani
jirgin saman daukar fasinjoji 71 da matukansa ya yi hadari wajen
saukarsa a filin jirgin sama Kathmandu (kasar Nepal). Mutane sama 50 ne
suka mutu lokacin da jirgin kirar Bombadier Dash 8 turboprop ya dumfari
taba kasa. 18 ga Fabriru: Wani
jirgin fasinjoji ya yi hadari a tsaunukan Zagros da ke Kasar Iran, inda
daukacin fasinjoji 66 suka halaka. Jirgin mallakar kamfanin sufuri na
Aseman Max Airlines ATR Jirgin kirar 'turboprop' ya yi hadari, inda
kimanin sa'a guda bayan tashinsa daga baban birnin kasar, Tehran lokacin
da ya nufi birni da ke Kudu maso yammacin kasar, Yasuj. 11 ga Fabrairu:
Wani jirgin fasinjan Rasha ya yi hadari mintuna kadan da tashinsa daga
filin jirgin saman Domodedovo da ke Mosko tare da fasinjoji 71, jirgin
kirar Antonovo An-148, mallakar kamfanin sufuri na Orsk a tsaunukan
Ural, lokacin day a yi hadari a kauyen Argunovo, kimanin kilomita 80
(mil 50) da ke Kudu maso Gabashin Mosoko.
2017
Ba
a samu hadrin jirgin sama a shekarar 2017 - wato wannan shekara ce da
ta kasance mai kariyar aukuwar hadarin jiragen sufurin saman a tarihi.
2016
25 ga Disamba: Wani
jirgin saman sojan Rasha kirar Tu-154 jet Ailiner ya yi hadari a tekun
Black Sea, inda aka samu asarar rayuka 92 tare da matukan jirgin.
Jirgin
ya rikito ne kasa jim kadan da tashinsa sama a wani filin jirgin sama
da ke kusa da birnin Sochi. Jirgin na dauke ne a 'yan wasa wanda aka
shirya za su yi wa rundunar sojan Rasha da ke Siriya kade-kade da
raye-raye, tare da ''yan jarida da sojoji.
Hakkin mallakar hotoEPAImage caption
Jirgin na dauke ne a 'yan wasa wanda aka shirya za
su yi wa rundunar sojan Rasha da ke Siriya kade-kade da raye-raye, tare
da ''yan jarida da sojoji
7 ga Disamba: Daukacin mutane 48 da
ke cikin jirgin fasinjan kasar Pakistan na PIA sun halaka lokacin da
jirgin ya yi hadari a Arewacin kasar.
Jirgin mallakar kasar tuni
daman an yi fama da shi kan kin tabbatar da matakan kariya - inda daga
bisani aka jajirce kan cewa sai an binciki jirgi mai lamba PK-661 wanda
ya taso daga Chitral zuwa Islamabad ba, wanda ba a same shi da nuna wata
alama ta matsalar inji a tattare da shi ba.
Hakkin mallakar hotoEPAImage caption
Daukacin mutane 48 da ke cikin jirgin fasinjan kasar
Pakistan na PIA sun halaka lokacin da jirgin ya yi hadari a Arewacin
kasar
28ga Nuwamba: Jirgin
da ke dauke da kungiyar 'yan kwallon kafar Brazil kulo din Chapecoen
mai ya kare masa, inda ya rikito a Medelin da ke Colombia ya halaka
mutane 71,. wadanda suka hada da ''yan wasa da jami'an gudanar da kulob
din. sai dai ''yan wasa uku na cikin wadanda suka tsira mutum shida,
yayin da wasu mutane tara (daga cikin''yan wasan) kuwa daman ba su samu
yin tafiyar ba. 19 ga Mayu:Shugaban
kasar Faransa Francois Hollande ya tabbatar da hadarin jirgin saman
Masar Egypt Air, wanda aka bayar da rahoton bacewarsa a tsakanin Parsi
da Cairo, inda ya yi hadari ya halaka mutane 66 da ke cikinsa. 19 ga Maris:
Wani jirgin FlyDubai kirar Boeing 737-800 ya yi hadari a Rostov-on-Don
da ke kasar Rasha, inda ya halaka daukacin mutane 62 da ke cikinsa.
2015
31 ga Oktoba:
Wani jirgi kirar An AirbusA321 mallakar kamfanin sufurin jiragen saman
Rasha Kogalymav ya yi hadari inda ya rikito adaga saman tsaunin Sinai da
kimanin mintuna 22 da dagawarsa sama bayan tasowarsa daga Sharm
el-Sheikh, inda ya halaka daukacin mutane 224 da ke cikinsa. Kungiyar
fafutikar Musulunci ta da ke yankin ta yi ikirarin kado da jirgin don
daukar fansa kan daukin da Rasha ta kai kasar Siriya. 30 ga Yuni: Jirgin
saman sojan Indonesiya kirar Hercules C-130 na sufuri ya yi hadari a
wata unguwa d aMedan. Jami'an soja sun ce daukacin mutane 122 da ke
cikin jirgin duk sun mutu, tare da wasu mutane 19 da hadarin ya rutsa da
su a kasa. 24 ga Maris: Jirgin sama kirar
Germanwings Airbus A320 ya yi hadari a tsaunukan Alps kusa da Digne
lokacin da ya tashi daga Barcelona zuwa Dusse. Daukacin mutane 148 da
ke cikin jirgin an shiga fargabar mutuwarsu.
2014
28 ga Disambar: Jirgin
sama kirar AirAsia QZ8501 da ya taso daga Surabaya da ke kasar
Indonesiya zuwa Singapore ya bace a tekun Java. matukin jirgin ya yiwo
wayar neman izinin karkata akalar tafiyar jirgin bisa dalilan munin
yanayi, amma bai samu amsa ba. a cikinsa akwai fasinjoji 162 tare da
masu aikin kula da su. 24 ga Yulin: Jirgin saman
kasar Aljeriya na Air Algerie mai lamba AH5017 ya bace a sararin
samaniyar kasar Mali daidai lokacin da aka yi fama da munin yanayi a kan
iyakar kasar da Burkina Faso jirgin kirar e McDonnell Douglas MD-8
mallakar kamfanin kasar Spain ne na Swiftair, sannan ya hjnufin birnin
Ouagadougou daga Algiers dauke da fasinjoji 116, 51 daga cikinsu
Faransawa ne. Daukacinsu dai duk an kaddara mutuwarsu. 23 gaYuli:
Mutum 48 sun mutu lokacin da wani jirgin saman kasar Taiwan na
Taiwanese ATR-72 ya yi hadari a wani teku da ya yi toroko lokacin da
jirgin ya tashi ba da dadewa ba.
Shi ma wani jirgin TransAsia
Airways GE222 dauke da fasinjoji 54 da masu kula da fasinjoji hudu da
suka nufi tsibirin Penghu. Ya yi yunkurin karkatar da akalarsa daga
sauka kasa kafin ya yi hadari dakika guda da yunkurin.
Hakkin mallakar hotoGetty ImagesImage caption
Jirgin sama mallakar kasar Malesiya na MH17 ya yi
hadari a kusa da garin Grabove da ke gabashin kasar Ukraine, ind aya
halaka daukacin mutane 298 da ke cikinsa
17 ga Yuli: Jirgin sama mallakar
kasar Malesiya na MH17 ya yi hadari a kusa da garin Grabove da ke
gabashin kasar Ukraine, ind aya halaka daukacin mutane 298 da ke
cikinsa, kuma mutane 193 daga cikin ;'yan tawagen Dutc ne da ke goyon
bayan Rasha wadanda aka zarge su da harbin jirgin suka kakkabo shi kasa,
ta hanyar amfani da makami mai linzami, sai dia sun musanta aikat
ahakan. 8 ga Maris: Jirgin sufurin saman kasar
Malesiya na MH370 wanda ya tashi daga birnin Kuala Lumpur zuwa Beijing
ya bace, al'amarin da ya haifar da bazama nemansa ka'in da na'in wanda
ba a taba yin irinsa ba a tsawon tarihi hada-hadar sufurin jiragen
sama.. Duk da irin dimbin kokarin da aka yi, musamman a yanki mai
mawuyacin hali na Kudancin tekun Indiya, babu abin da aka gano har zuwa
yulin 2015, yayin da da ruwa ya turo fuffuken jirgin waje a kan tsibirin
Reunion. Jami'an gwamnatin Faransa sun tabbatar da cewa an samu
buraguzan jirgin MH370 (da ya yi batan dabo). 11 ga Fabrairu:
Wani jirgin daukar kaya na soja samfurin a Hercules C-1 dauke da
mutajne 78 ya yi hadari a wani yankin tsaunukan Arewa maso Gabashin
Aljeriya. Rahotanni sun nuna cewea mutum daya ne ya tsira daga jami'an
sojan, daga iyalan soja da matukan jirgin.
2013
17 ga Nuwamba: Jirgin
Kamfanin sufurin jiragen sama na Tatarstan kirar Boeing 737 ya yi
hadari lokacin saukarsa a Kazan da ke kasar Rasha, inda ya halaka
daukacin mutane 50 da ke cikinsa. 16 ga Oktoba:
Mutane arba'in da tara, wadanda suka hada da 'yan kasar waje da suka
fito da kimanin kasashe 10, tare da 'yan kasar Laotian, sun mutu ya yin
da jirgin sufurin saman Lao Airlines aTR 72-600 ya tsunduma cikin kogin
Mekong lokacin da ya yi yunkurin sauka.
2012
3 ga Yuni: Jirgin
sufuri na Dana Air dauke da fasinjoji 150 ya yi hadari a wani yanki da
ke cunkushe da jama na birni mafi girma a Najeriya, wato Legas. 20 ga Afirilu:Wani
jirgin saman A Bhoja Air kirar Boeing 737 ya yi hadari lokacin da ya
kusa isa filin jiragen saman babban birnin Pakistan Islamabad, inda ya
halaka daukacin fasinjoji 121 da matukansa su shida.
2011
26 ga Yuli: Wasu
mutane 78 sun halaka a hadrin jirgin saman sojan kasar Moroko kirar
C-130 Hercules wanda ya yi hadari a tsaunin da ke kusa da Guelmin da ke
kasar Moroko. Jami'an Gwamnatin Moroko sun dora alhakin aukuwar hadar
kan mummunan yanayi.
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Matukan jirgin sun kai rahoto matsalatr inji kafin sun yi yunkurin sauka kasa
8 ga Yuli: Jirgin sufurin sama na
Hewa Bora Airwa ya yi hadari sanadiyyar mumunan yanayi a Jamhuriyar
Dimokuradiyyar Kongo, inda mutane 74 suka halaka daga cikin mutane 118
da ke cikin jirgin. 9 ga Janairu: Jirgin sufurin
saman kasar Iran IranAir kirar Boeing 727 ya babbale gutsi-gutsi a kusa
da birnin Orumiyeh, inda mutane 77 suka mutu daga cikin mutane 100 da ke
cikin jirgin.
Matukan jirgin sun kai rahoto matsalatr inji kafin sun yi yunkurin sauka kasa.
2010
5 ga Nuwamba:
Jirgin fasinjan Aerocaribbean kirar turboprop ya yi hadari a tsaunukan
da ke tsakiyar kasar Cuba, inda daukacin mutane 68 da ke cikin jirgin
suka mutu. 28 ga Yuli: Jirgin saman hada-hadar
sufurin cikin gida na kasar Pakistan Airblue da ya taso daga birnin
Karachi ya yi hadari a wani gabar dutse yayin da ya yi yunkurin sauka a
filin jiragen saman Islamabad, inda ya halaka daukacin mutane 152 da ke
cikinsa. 22 ga Mayu: Jirgin saman sufurin kasar
Indiya na Air India Express Boeing 737 yyin da ya haure saman wani dutse
a filin jirgin saman Manglore da ke kudnacin Indiya, sai ya yi hadari a
gabar wani dutse, inda ya kama da wuta , inda ya halaka mutun 158. 12 ga Mayu: Jirgin
saman sufuri na kasar Libiya Afriqiyah Airways kirar Airbus 330 yayin
da ya yi yunkurin sauka afilin jirgin saman Tripoli da ke kasar Libiya,
ind aya halaka sama da mutum 100. 10 ga Afirilu:
Wani jirgi kirar Tupolev 154 dauke shugaban kasar Poland Lech Kaczynski
ya yi hadari a kusa da filin jiragen saman Rasha na Smolensk, inda sama
da mutane 90 da ke cikinsa suka mutu. 25 ga Janairu:
Jirgin sufurin saman kasar Habasha mai duakar fasinjoji na Ethiopian
Airlines ya afka cikin teku tare da mutane 89 da ke cikinsa jim kadan da
tasowarsa daga birnin Beirut (na kasr Lebanon)
2009
15 ga Yuli:
Jirgin saman sufurin Caspian Airlines samfurin Tupole ya yi hadari a
Arewacin kasar Iran yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Armenia. Daukacin
fasinjoji 168 da matukansa an bayar da rahoton mutuwarsu. 30 ga Yuni:
jirgin saman safar fasinja na kasar Yemen kirar Airbus 310 ya yi hadari
inda ya afka tekun Indiya kusa da tsaunukan Comoros archipelago. mutum
daya ne daga cikin mutane 153 da ke cikin jirgin ya tsira. 1 ga Yuni: Jirgin
sufurin saman Faransa kirar Airbus 330 da ya taso daga birnin Rio de
Janeiro zuwa Paris ya yi hadari inda ya afka tekun Atlantic tare da
mutane 228 da ke cikinsa. Daga bisani masu aikin ceto sun lalubo
gawarwakin mutane 50 a cikin tekun.
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Jirgin saman sojan kasar Indonesiya kirar C-130
Hercules mai dakon kaya ya yi hadari a kauyen da ke gabashin Java, inda
akala mutane 97 suka halaka.
20 ga Mayu: Jirgin saman sojan
kasar Indonesiya kirar C-130 Hercules mai dakon kaya ya yi hadari a
kauyen da ke gabashin Java, inda akala mutane 97 suka halaka. 12 ga Fabrairu:Jirgin
fasinja ya yi hadari a wnai gida da ke Buffalo, a birnin New York (da
ke kasar Amurka), inda dukacin mutane 49 da ke cikinsa da wani mutum
guda da hadarin jirgin ya rutsa da shi a kasa har ya mutu. 2008 14 ga Satumba:
Wani jirgi kirar Boeing-737 da ya yi hadari lokacin saukarsa a kusa da
wani birni na Perm da ke tsakiyar kasar Rasha, inda ya halaka daukacin
fasinjoji 88 da matukansa da ke ciki. 24 ga Agusta: Wani jirgin fasinja ya yi hadari jim kadan da tashinsa daga Bishkek babban birnin Kyrgyzstan, inda ya halaka mutane 68. 20 ga Agusta: Jirgin
saman ksar Spain ya karkace wa titin yunkurin tashin jiragen sama a
filin jiragen saman Madrid Barajas, inda ya halaka mutane 154, tare da
jikkata wasu mutane 18 da suka samu raunuka. 2007 30 ga Nuwamba:
Daukacin mutane 56 da ke cikin hjirgin saman Atlasjet sun mutu lokacin
da jirgin ya yi hadari a kusa da garin Keciborlu a yankin tsaunukan
Lardin Isparta, da ke kimanin kilomita 12 (mil 7.5) daga filin jiragen
saman Isparta. 16 ga Satumba: Akalla mutane 87
suka mutu yayin da wani jirgin sama ya yi wata irin saukar harigido a
cikin mummunan yanayi a wajen shakatawa na Thailanda da ke Phuket. 17 ga Yuli:
Wani jirgin saman sufuri na kamfani TAM Airline ya yi hadari a wajen
saukarsa a filin jiragen saman Congonhas da ke Sao Paulo a kasar Brazil,
al'amarin da ya kasance mummunan hadarin jirgin saman da ba a taba yin
irinsa ba. Mutane 199 suka mutu - daukacin mutane 186 da wasu mutane 13
da hadarin ya rutsa da su a kasa. 5 ga Mayu:
Jirgin kamfanin sufurin saman kasar Kenya kirar Boeing 737-800 ya yi
hadari a harkakiyar ciyayin tabo da ke kudancin kasar Kamaru, inda
daukacin mutane 114 da ke cikinsa suka mutu. Binciken da jami'ai suka
gudanar har yanzu bai bayar da musababbin hadarin ba. 1 ga Janairu:
Wani jirgin sufurin saman Adam Air kirar Boeing 737-400 dauke da
fasinjoji 102 da matukansa ya fado kan tsaunukan da ke tsibirin Sulawesi
a sufurin cikin gida da ya gudanar a kasar Indonesiya. Daukacin wadanda
ke cikin jirgin duk sun mutu. 2006 29 ga Satumba:
Wani jirgi kirar Boeing 737 dauke da fasinjoji 154 tare da matukansa y
yi hadari a dajin Amazon da ke kasar Brazil, inda dukacin mutanen da ke
cikins asuka mutu, bayan da ya yi karo da wani babban jirgi a tsakiyar
sararin samaniya. 22 ga Agusta: Wani jirgin kasar Rasha kirar Tupolev-154 dauke da fasinjoji 170 ya yi hadari a Arewacin Donetsk da ke gabashin Ukrain. 9 ga Yuli:
Wani jirgin kasar Rasha samfurin Russian S7 kirar Airbus A-31 ya sauka
daga titin tashin jiragen sama lokacin da ya sauka a filin jiragen
saman Irkutsk da ke Siberia. Kimanin mutane 124 da ke cikin jirgin sun
mutu, amma fiye da mutum 50 sun tsira. 3 ga Mayu:
Wani jirgin Armavia kirar Airbus A-320 ya yi hadari a tekun Black Sea
kusa da Sochi, inda daukacin mutane 113 da ke cikinsa suka mutu. 2005 10 ga Disamba:
Wani jirgin sufuri na Sosoliso Airlines DC-9 ya yi hadari a birnin
Fatakwal da ke Kudancin Najeriya, inda ya halaka mutane 103 da ke
cikinsa. 6 ga Disamba: Wani jirgin soja kirar
AC-130 na sufuri ya yi hadari a wajen babban birnin kasar Iran, Tehran,
inda mutane 110 da ke cikinsa, tare da wasu da hadarin ya rutsa da su a
kasa.
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Wani jirgin sufuri na Mandala Airlines dauke da
fasinjoji 112 da matukansa mutum biyar ya yi hadari bayan tashinsa daga
birnin Medan da ke kasar Indonesiya
22 ga Oktoba: Wani jirgin sufuri na
Bellview airlines kirar Boeing 737 dauke da mutane 117 da ke cikinsa
ya yi hadari bayan tashinsa daga birnin Legas da ke Najeriya, inda ya
halaka duk wanda ke cikinsa. 5 ga Satumba: Wani
jirgin sufuri na Mandala Airlines dauke da fasinjoji 112 da matukansa
mutum biyar ya yi hadari bayan tashinsa daga birnin Medan da ke kasar
Indonesiya, inda ya halaka daukacin mutanen da ke cikinsa, tare da wasu
da hadarin ya rutsa da su a kasa. 16 ga Agusta:
Wani jirgin kasar Columbia na kamfanin sufurin West Caribbean Airways ya
yi hadari a wata karkara da ke kasar venezuela, inda daukacin mutane
160 da ke cikinsa suka halaka. Jirgin wanda ya tunkari kasar Panama zuwa
Martinique, an ajiye shi a wata unguwa da ke tsibirin Carribbean. 14 ga Agusta:
Jirgin sufurin kamfanin Helios Airways ya taso daga Cyprus zuwa Athens
dauke da mutane 121 ya yi hadari a Arewaci babban birnin kasar Girka,
Athens, nan take bayan ya yi sako-sakon rashin karfin da ke rikonsa a
sama. 16 ga Yuli: Jirgin sufuri na Equatair ya
yi hadari nan take da tashinsa daga tsibirin babban birnin kasar
Equatorial Guinea, Malabo, da ke Yammacin kasar, inda daukacin mutane 60
da ke ciki suka mutu. 3 ga Fabrairu: An gano
buraguzan balgataccen jirgin Kam Air kirar Boeing 737 a manyan
tsaunukan da ke kusa da birnin Kabul na kasar Afghanistan, kwanaki biyu
bayan da jirgin ya bace wa na'urar bin kadin tafiyarsa a cikin yanayin
zubar kankara. Daukacin mutane 104 da ke cikinsa an ce sun mutu. 2004 21 ga Nuwamba: Jirgin
saman fasinja ya afka cikin tafkin kankara da ke kusa da birnin Bbaotou
da ke can cikin yankin Mangolia da ke Arewacin kasar Sin, inda daukacin
mutane 53 da ke cikin jirgin suka halaka, tare da wasu mutane biyu da
hadarin ya rutsa da su, kamar yadda jami'an hukuma suka bayyana. 3 ga Janairu: Jirgin
sufurin saman Masar mallakar kamfanin sufurin jiragen sama na Flash
Airlines ya fada cikin tekun Red Sea, inda daukacin mutane 141 da ke
cikinsa suka mutu. Mafi yawan fasinjojin ana da tabbacin ''yan yawon
bude ido ne daga kasar Faransa. 2003 25 ga Disamba: Wani
jirgi kirar Boeing 72 ya yi hadari daga tashinsa daga kasar Benin da
ke yankin Afirka ta Yamma, inda ya halaka akalla mutane 135 da ke kan
hanyarsu ta zuwa Lebanon. 8 ga Yuli: Wani jirgi
kirar Boeing 72 ya yi hadari a Sudan jim kadan da tashinsa, inda ya
halaka mutane 115 da ke cikinsa. Fasinja daya ne da wani jariri suka
tsira.
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Hatsarin jirgi a Jamhuriyar Benin mai samfurin
Boeing 727 ya fado jim kadan da tashinsa dropped out of the sky soon
after take-off, killing at least 135 people travelling to Lebanon
26 ga Mayu: Jirgin saman Ukrainian
Yak-42 ya yi hadari kusa da wurin shakatawa na tekun Black Sea na
Trabzon da Arewa maso yammacin Turkiyya, inda ya halaka daukacin mutane
74 da ke cikinsa - kuma mafi yawancinsu masu aikin tabbatar da zaman
lafiya da suka fito daga kasar Spain yayin da suke komowa gida daga
kasar Afghanistan. 8 ga Mayu: Kimani mutane 170
ne aka bayar da rahoton mutuwarsu a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo
bayan da wani tsohon jirgin sufurin saman Rasha na dakon kaya ya afka
musu, wato kirar Ilyushin 76 na dakon kaya, wanda kai-tsaye ya afka musu
ya sunkucesu ya watsar waje. 6 ga Maris: Wani
jirgin saman Algeria kirar Boeing 737 ya yi hadari bayan tashinsa daga
filin jirgin saman Tamanrasset, inda kimanin mutane 102 suka mutu. 19 ga Fabrairu:
Wani jirgin saman soja na kasar Iran na sufuri dauke da mutane 276 ya
yi hadari a kudancin kasar, inda dukacin mutanen cikinsa suka mutu. 8 ga Janairu:
Wani jirgin sufurin Turkiya na Turkish Airlines A Turkish Airlines
dauke da fasinjoji 76 tare da matukansa ya yi hadari yayin da yake
kokarin sauka a Diyarbakir. 2002 23 ga Disamba:
Wani jirgin sufuri na Antonov 140 dauke da kwararrun masana harkar
hada-hadar jiragen sama ya yi hadari a tsakiyar kasar Iran, inda ya
halaka daukacin mutane 46 da ke cikinsa. Tawagar masana sun yi tafiyar
da zimmar nazarin yadda za su inganta irin wannan jirgin da Iran ta kera
bayan da aka ba ta lasisin izinin yin hakan. 27 ga Yuli: Wani
jirgin yaki ya yi hadari inda ya fada cikin taron jama'a 'yan kallon
wasa da ke wani gari a Yammacin kasar Ukrain na Lviv, inda ya halaka
mutane 77, al'amarin da aka yi nuni da cewa shi ne hadarin jirgin sama
mafi muni a duniya. 1 ga Yuli: mutane saba'in da
daya, wadanda mafi yawansu kananan yara lokacin da jirgin Rasha kirar
Tupolev 154 ya yi hadari a wata tafiya da 'yan makaranta suka yi zuwa
kasar Spaijn a jirgin sama kirar Boeing 757 na sufuri da ya yi karo da
jirgin a kudancin Jamus. 25 ga Mayu: Jirgin swama
kirar Boeing 747 mallkar kassar Taiwan na China Airlines ya yi hadari
inda ya afka cikin teku kusa da tsibirin Penghu da ke kasar Taiwan, tare
da fasinjoji 225 da matukansa. 7 ga Mayu: Jirgin
saman kamfanin sufurin jiragen sama na China Northern Airlines plane
dauke da mutane 112 ya afka cikin teku kusa Dalian a Arewa maso Gabashin
kasar Sin. 7 ga Mayu: Irin wannan ranar dai,
Jirgin sufurin saman kasar Masar na EgyptAir kirar Boeing 735 ya yi wata
irin saukar harigido a kusa da Tunis (babban birnin Tunusiya) tare da
fasinjoji 55 da matukansa mutum 10. Mafi yawan mutanen duk sun tsira
daga wannan kwarya-kwaryan hadari. 4 ga Mayu:
Wani jirgin sama kirar A BAC1-11-500 mallakar EAS Airlines ya yi hadari a
birnin Kano da ke Najeriya, inda ya halaka mutane 148 - kimanin rabinsu
hadarin ya rutsa da su ne a kasa. 15 ga Afirilu:
Jirgin sufurin kasar Sin na Air China flight 129 ya yi hadari lokacin
da yake kusantar Pusan da ke kasar Koriya ta Kudu, tare da da fasinjoji
160 da matukansa. 12 ga Fabraru: Wani jirgin sama
kirar Tupolev 154 mallakar kamfnain sufuri na Iran Air ya yi hadari a
tsaunukan Yammacin kasar Iran, inda ya halaka daukacin mutane 117 da ke
cikinsa. 29 ga Janairu: Wani jirgin sama kirar
Boeing 727 na kamfanin sufurin jiragen saman kasar Ecuadore na TAME
Airline ya yi hadari a tsaunukan da ke kasar Colombiya, inda ya halaka
mutane 92 da ke cikinsa. 2001 12 Nuwamba:
Jirgin sufurin saman Amurkawa na American Airlines kirar A-300 mai zuwa
Jamhuriyar Dominican ya yi hadari bayan tashinsa daga wata unguwa da ke
Borough na Queens da ke New York, inda daukacin mutane 260 suka halaka,
tare da wasu mutane biyar da hadarin ya rutsa da su a kasa. 8 ga Oktoba:
Wani jirgin sufurin yankin Scandinavia na Scandinavian Airlines System
(SAS) ya yi taho-mu-gama da wani karamin jirgin sama a yayin matsanancin
hazo da ke kan titi tashin jirgin sama na filin jirgin saman Milan
Linate, inda ya halaka mutane 118 da ke cikin jirgin.
Hakkin mallakar hotoGetty Images4 ga Oktoba: Jirgin sufurin saman
Rasha na Russian Sibir Airlines kirar Tupolev 154 da ke kan hanyarsa ta
zuwa Tel Aviv (babban birnin kasar Isra'ila) zuwa Novosibirsk a Siberia
(wani yanki na kasar Rasha), yayin da ya raba tsaka a sararin samaniya
sai ya yi bindiga ya tarwatse ya fada cikin tekun Black Sea, inda ya
halaka fasinjoji 78 da matukansa. 3 ga Yuli: Jirgin
saman Rasha kirar Tupolev 154 da ke kan hanyarsa ta zuwa Yekaterinburg
da ke tsaunukan Ural da ke kaiwa zuwa ga tashar jiragen ruwan Rasha
na Vladivostok, inda ya fada birnin Siberia a garin Irkutsk, inda
fasinjoji 133 da masu kula da fasinjojin 10 suka halaka. 2000 30 ga Oktoba: Jirgin
sufurin saman kasar Singapore Airlines kirar Boeing 747 da ya tashi
zuwa Los Angeles ya yi hadari daga tashinsa a filin jiragen saman Taipei
da ke kasar Taiwan, inda ya halaka mutane 78 daga cikin mutanen 179 da
ke cikinsa. 25 ga Yuli: Jirgin saman Faransa na
Air France Concorde da ke kan hanayarsa ta zuwa New York ya yi hadari
inda ya fada wani Otal da ke wajen birnin Paris jim kadan da tashinsa,
inda ya halaka mutane 113, wadanda suka hada da wasu mutane hudu da
hadarin ya rutsa da su a kasa.
Hakkin mallakar hotoGetty ImagesImage caption
Jirgin sufurin saman kasar Singapore Airlines kirar
Boeing 747 da ya tashi zuwa Los Angeles ya yi hadari daga tashinsa a
filin jiragen saman Taipei da ke kasar Taiwan
17 ga Yuli:Jirgin
saman Alliance Air kirar Boeing 737-200 ya fada kan wasu gidaje yayin da
yake kokarin sauka a Patna da ke kasar India, inda ya kashe mutane 51
da ke cikinsa tare da wsu mutane hudu da ke kasa. 19 ga Afirilu:
Jirgin saman Air Philippines kirar Boeing 737-200 wanda ya tashi daga
Manila zuwa Davao daf da saukarsa kasa ya yi hadari, inda ya halaka
daukacin mutane 131 da ke cikin jirgin. 31 ga Janairu:
Jirgin sufurin saman Alaska Airlines MD-83 wanda ya taso daga kasar
Mexico zuwa San Francisco (na kasar Amurka) ya fada cikin teku da ke
gabar Kudancin California, inda daukacin mutane 88 da ke cikin jirgin
suka halaka. 30 ga Janairu: Jirgin sufurin sama
na kasar Kenya mallakar Kenya Airways kirar A-310 ya fada cikin tekun
Atlantic jim kadan da tasowarsa daga Abidjan da ke kasar Ivory Coast, a
kan hanyarsa ta zuwa Legas a Najeriya. Daukacin mutane 179 ban da mutum
10 da ke cikin jirgin sun mutu. 1999 31 ga Oktoba:
Jirgin saman sufurin kasar Masar na EgyptAir kirar Boeing 767 ya yi
hadari a tekun Atlantic bayan da ya taso daga filin jiragen saman John
F. Kennedy da ke New York da zimmar zuwa Cairo babban birnin kasar
Masar, inda ya halaka daukacin mutane 217 da ke cikinsa. 24 ga Fabrairu:
Jirgin sufuri na kamfanin China Southwest Airlines y yi hadari a gabar
ruwan kasar Sin Lardin Zhejiang bayan da ya raba tsakiya a sararin
samaniya sai ya yi bindiga (ya fashe). Daukacin mutane 61 da ke cikin
jirgin kirar Rasha samfurin TU-154, wanda ya taso daga Chongqing zuwa
Kudu masio gabashin birnin Wenzhou duk mutanen ciki sun mutu. 1998 11 ga Disamba:
Jirgin sufurin kasar Thailand na Thai Airways International kirar A-310
ya yi hadari a sufurin cikin gida lokacin yunkurinsa na uku wajen suaka
a Surat Thani da ke Thailand, inda ya halaka mutane 101. 2 ga Satumba:
Jirgin sufurin saman kasar Switzerland na Swissair MD-11 da ya taso
daga New York zuwa Geneva sai ya yi hadari a tekun Atlantic da ke gefen
kasar Kanada, inda ya halaka daukacin mutane 229 da ke cikin jirgin. 16 ga Fabrairu:
Jirgin saman sufuri kirar Airbus A-300 mallakar kamfanin sufuri na
Taiwan's China Airlines ya yi hadari a filin jirgin sama da ke kusa da
Taipei Chiang Kai-shek yayin da ya yi yunkurin suaka a yanayin hazo da
ruwan sama bayan da jirgin ya taso daga Bali da ke kasar Indonesiya.
Daukacin mutane 196 da ke cikinsa tare da wasu mutane bakwai da ke kasa
duk sun mutu. 2 ga Fabrairu: Jirgin saman kasar
Philippines na Cebu Pacific Air DC-9 ya yi hadari a tsaunukan da ke
kudancin kasar Philippines, inda ya halaka daukacin mutane 104 da ke
cikinsa.