Da wayar salula zaka iya magana da mutum ako ina aduk fadin duniyarnan,amma kasan yadda take wannan aikin kuwa?
Wayar salula tanada wani abu mesuna two-way radio,abun nufi shine tana iya ansa da kuma bayar da sigina ta sadarwa na hasken maganadisun lantarki.
Wato ita salula tana daukene da abunda ke turawa dakuma ansar sigina.
Duk lokacin da mukeyin waya,salula tana canza sautin muryarmu zuwa sigina ta lantarki(electrical wave) wanda shine zetafi a yanayin hasken maganadisun lantarki zuwa towa kokuma karfen sabis.
Sannan shikuma wannan towa din seya turashi zuwa wani towa din ayanayin sigina ta maganadisun rediyo(radio wave) ahaka harzuwa wanda muke wayar dashi.
Sannan ita kuma wayar salulan abokin wayarmu ta ansa wanda sigina din kuma ta canza shi zuwa hasken maganadisun lantarki(electrical wave) sannan kuma tamaida shi zuwa sautin magana wanda abokin wayarmu zeji.
Wayar salula dile setana dauke da antena wadda itace dake canza siginar rediyo zuwa ta labtarki .Labels: Fasahar Na'ura, Kimiyya da fasaha