Ita amana wata abuce wadda mutane sukafi kaunarta ballema ace masoya,ita cin amana wata abuce wadda akasarin mutane sun tsaneta musamman masoyan gaskiya.
Ita soyayyar gaskiya atsakanin mutane ake samunta amma ba dukkanin mutanene suke kamantataba,kuma bakasanin mesonka acikin yan uwanka,abokai harma iyayenka harse wani abun damuwa,farinciki ko bakinciki yafaru dakai.
Kasance me rikon amana kodan mahaliccin ka domin ita duniya batada tabbas.
Rayuwar duniya taxama wani abu wanda yawancin mutane suna nuna soyayyane domin arziki ko wani abun duniya,zakaga anason mutum lokacin da yakeda arziki amma dazaran bayidashi sekaga an kyaleshi.
Kasance me nuna so domin mahaliccinka domin ita soyayyar gaskiya a kullum kara mana tausayi takeyi.
Balefi bane ka kwada mai sonka tahanyar nuna wani abu da muka mallaka daga baya kuma semu nuna babu wannan abun duk da wecan munsan ita zuciyar akullum tanason me kautatamata
Masu iya magana sunce aboki shine zenuna soyayya akoda yaushe amma seya kasance dan uwa alokacin da damuwa tasamemu.
Wani lokaci sekaga wanda akekira da aboki yaganka xakashiga matsala amma baze hanakaba sebayan matsalar tafaru seyazo yanacewa ainaso nahanaka amma naji tsoron cewa bazaka so hakanba,shiko abokin gaskiya akoda yaushe xegayama gaskiyane koda bazakaji dadin hakan ba.
Nidai fatana mukasance masu rikon amana a rayuwa domin musamu dacewa.Labels: Soyayya