Duk dacewa Ronaldo yatabacewa ze bugawa Madrid kwallo har karshen wa'adinshi na kwallo amma
Rahotanni masu karfi na kara bayyana cewar
komawar tauraron dan kwallon kafa, Cristiano
Ronaldo kungiyar Juventus daga Real Madrid,
da safiyar yau wata jarida me suna Records ta
ruwaito cewa an yi zama tsakanin me
kungiyar Real Madrid, Florentino Perez da
wakilin Ronaldo inda sakamakon zaman ya
bayyana cewa Ronaldo ya riga ya juyawa
Madrid baya.
Ronaldo dai zaisa hannu a takardar yarjejeniyar buga mata
kwallo har zuwa shekarar 2022 akan albashin
Yuro miliyan talatin(£30m) duk shekara.
Haka shima wani tsohon me horas da ‘yan
wasa na kungiyar Juventus din me sun Moggi
ya bayyanawa wani gidan talabijin din kasar
Italiya cewa bayanan da yake dasu sun
tabbatar mai da cewa Ronaldo ya rigaya ya
sakawa Juventus hannu akan takarda dan
buga mata wasa, dan tuni an gama mai gwajin
lafiya da sauransu.
Itama jaridar AS ta ruwaito cewa nan da
awanni kadanne Ronaldon zai sakawa Juventus
hannu a yarjejeniyar buga mata wasa kuma
zasu sayi Ronaldonne akan kudi Yuro miliyan
dari.
Ronaldo dai ya taba bayyana cewa, lokacin yana
yaro yaso bugawa Juventus wasa, kuma a
lokacin da yaci juventus kwallonnan ta watsiya
a lokacin buga gasar cin kofin turai, bayan
kammala wasan ya godewa masoya kungiyar
da jinjina mai da sukayi.
Ronaldo yakaradacewa Juventus ce kawai zata iya bashi damar kara cin kofin champoion league bayan biyar da yaci a United dakuma Madrid.
Sannan kuma anji dan kwallo wato Matuidi yanacewa zuwan Ronaldo Juventus zezamo babbar nasara.
Toh abundai yakara hargitsewa alokacin da Ronaldo ke kokarin komawa Juventus sukuma Madrid suna fafitikar neman wanda ze biye gurbinsa.
Toh atakaice dai Juventus setabiya Madrid kudi kimanin Miliyan dari da sha bakwai a dalar amurka($117m) kokuma Yuri miliyan dari(£100m).
Yanzu dai lokaci za’a jira a ga yanda lamurra
zasu wanye.Labels: Labarai