SOYAYYA TAKAISHI GIDAN YARI

Wani matashi yatafi gidan yari sakamakon bayyana soyayyarsa ga wata yar majalisa mesuna Ms Rwabwoogo.
Anyankewa wannan matashin zaman gidan kaso harna shekara biyu domin bayyana soyayya ga yar majalisan.
Matashin dan shekaru 25 dalibine a kasar Uganda wanda ake kira da Brian Isiko,anyi zarginsa da kalamai marasa dadi da wasu da basu daceba bayan nuna soyayya ga yar majalisan.
Matashin dai ya tabbatar da cewa sakonnin da kiraye kirayen waya duk daga gareshine.
Itadai wannan yar siyasan ta gayawa kotu cewa tafara samun sakonnin soyayya daga wanda batasani ba tun a watan November na shekarar 2017 wanda hakan yasa taji cewa wani naso yacutar da uta.
Tayi tunanin abun wasane sekuma taga abun bana kare bane harma taje ganin tarko ne don amuzanta mata .
Hakan shiyasa tagawa yan sanda,takara dacewa abunda yafi sakon daya matukar kona mata rai shine wanda ke cewa "ina sonki sosai kuma inaso in kareko,sotayyata takice kuma na lura bakida mw kula dake don haka zanzamo me kulawa dake domin nasan kina cikin matsala"
Tafada cewa lakacin da suka hadu dashi yanuna mata ID card dinsa sannan masu tsaron ta suka kamashi.
Ms kamasanyu tabadashi shekara biyu a gidan yari domin kuntatamata dayayi sannan kuma wata tara domin magana dayayi da ita tahanyar da bata daceba.

Labels: