SHIN MEYASA KIFI YAKE WARI INMUKA SHIYOSHI KUMA YAZAMU CIRE WARIN

To anan dai kimiyyar chemistry ce zata gayamana dalilin da kifi yake wari inmuka siyoshi.
Dalilin dai shine akwai wani abun yanayi dayake faruwa ajikin fikin domin wasu sinadarai(molecules) da ake kira Bacterial Enzymes wainda suke shiga jikin naman kifin,to wannan seya jawo abkuwar wani yanayi da akekira Oxidation Reaction.
Ita tsokar kifi tana daukene da wani sinadari mesuna Trimethylamine Oxide(TMAO) wanda idan ya narke bayan mutuwar kifi seya koma wasu sinadai guda biyu da ake kira da Trimethylamine dakuma Dimethylamine.

To wannan hadin sinadaran guda biyu shike kawo kifi yaringa wari,atakaice ma dai wannan Trimethylamine din dashi akegane kifi mekyau.
Amma kunsan kuwa cire wannan warin abune me matukar sauki?
Yadda zamu cire wannan warin shine tahanyar yin amfani da Lemon,Vinegar da kuma Baking Soda.
Dukkanin sinadaran damuka lissafo sunada wani yanayi da ake kira Alkaline Base Nature amma shikuma Lemon yanada yanayin Acid ne kuma dukkaninsu kishiyoyin junane to shiyasa lemon ze karya karfin wainnan sinadaran.
Shine ma yasa akesa lemon akifi.

Labels: