SHIN AKWAI SOYAYYAR HAR ABADA?

Itadai soyayya ana ginata ne akan dalilin wani abu da wanda mukeso yake dashi wannan ajinin mutum yake bawai wasu ne keyin hakan ba a'a kowa da kowane.
Wannan abun da mukeso ze iya zama kyau,ilimi,arziki,sarauta,hali ko kuma makamantansu.
To a gaskiyar magana mafi yawancin wainnan abubuwan basa zama tabbas a rayuwarmu,yan kalilan acikinsu zasu iya zamowa tabbas kamar ilimi kokuma halin mutum.
Ammafa shi halin mutum yana tafiyane da inda ya tsinci kanshi to kenan koda yaushe ze iya canzawa.
Gaskiyar magana dai soyayyar har abada bata yuwuwa domin in kaso mutum don kyawun da yake dasgi to bamakawa akwai tsufa kuma da zarar tazo babu maganar kyau.
Koma babu tsufa akwai rashin lafiya,accident ko wani abu wanda ze kaudar da wannan kyan.
To kenan soyayya domin kyau akoda yaushe zata iya karewa.
Udan kuma munyu soyayya domin arziki dukkaninmu munsan cewa arziki nupin Allah ne kuma bayida tabbas sega wanda Allah yaso.
To domin haka soyayya domin arziku ba soyayyar har abada bace.
Hakama soyayya domin sarauta bazata bata zama ta har abada ba domin ita sarautarma ta wani lokacice.
Soyayya domin hali zata iya zamowa ta har abada saboda halin mutum yakan iya dorewa har karshen rayuwarsa ama shi babu tabbacin hakan.
Abu mafi yuwuwa shine kawai soyayya domin ilimi don shi lilimi mafi yawancu baya karewa.
Ammafa ku sani shi kanshi ilimin ana iya rasashi domin mutum yana iya samun accident daganan yasamu tabuwa a kwakwalwa sannan daganan wannan ilimin za'a iya rasashi.
To atakaice dai bawata soyayya da zata iya zamowa ta har abada domin kowata soyayya tanada dalilin farata sannan kuma dukkanin wainna  dalilan bazasu taba zamowa mallakinmu na har abadaba.
Kawai dai inzamuyu soyayya muyita ta dan lokacin damukedashi domin koda anyi aure dalilin dayasa mukafara soyayyar ze iya karewa sede domin karfin da aure yakedashi wani dalilin ze bullo wanda ze tsayar da wannan  soyayyar domin shi aure ba abun wasa bane.
Mudena tinanin akwau wata soyayya da zata iya zama ta har abada domin indai zaka yiwa kanka ko kanki adalci indai kataba yin soyayya kuna ta rushe to zaka fahimci cewa bazaka iya son mutum har abada ba.
Wannan kawai yanayinmune na mutane kuma bawabda ze iya canzashi.

Labels: