NAJERIYA ZATAKAI KARAR LAFARI WAJEN FIFA

Ministan wasannin Najeriya, Solomon Dalung, ya ce ya
umarci hukumar kwallon kafa ta kasar (NFF), data
shigar da koke gaban hukumar kwallon kafa ta
duniya FIFA, kan yadda yace aka yiwa wasu kasashen Afirka rashin
adalci a gasar kofin duniya a Rasha.
Mista Dalung yace rashin adalci daga bangaren
alkalan wasa ne kuma shine musabbabin rashin nasarar 'yan
wasan kasashen Afirka wasanni da suka buga da kasashen
Croatia da Argentina.

*Da gaske ne an ba lafarin Najeriya da Argentina
kudi?
To komadai menene akayi kawai rashin adalci ne
Wasu 'yan Najeriya ba su ji dadin yadda alkalin
wasan Najeriya da Argentina ya ki bayar da fena'areti
ba duk da cewa bidiyo ya nuna yadda kwallo ta taba
hannun dan wasan Argentina
Sai dai kuma wasu suna ganin hukuncin da lafarin ya
yanke ya yi daidai.
To amma mafiyawancin yan Nijeriya sun yarda zewa koda ankai karar lafari wajen FIFA babu abunda za'ayi domin harda hadin bakin FIFA dakanta

Labels: