Wannan tambaya an dad’e ana kaiwa da kawowa a kanta, masana da yawa sun tattauna domin ganin sun samar da ma’anarta domin a gane ta a kuma fahimce ta. Kamar haka:
Soyayya ita ce nuna ‘kauna daga bangarori biyu na masu ‘kaunar juna
An bayyana soyayyar kamar haka
‘Soyayya ita ce ni’ima mafi d’aukaka da Allah Ya ba wa bayinsa. Soyayya ita ce zuciyoyi biyu a dun’kule su cure, su game cikin zuciya d’aya. Haka kuma soyayya ita ce rai biyu cikin jiki d’aya. Soyayya ita ce mutum biyu cikin mutum d’aya. Abin da ake nufi a nan shi ne, idan mutum ya so wani tsananin soyayya sai ya zama cewa koda yaushe cikin tunaninsa yake, ba ya damuwa da kowa sai shi, ba ya son ji da ganin kowa sai shi, wato kenan sun zama mutum d’aya cikin jiki biyu.’
Duk da abubuwan da muka ambata hakan ba zai sanya mu ce mun bayyana ha’ki’kanin ma’anar soyayya ba. Domin ita soyayya ba za a iya siffanta yadda take ba. Sai mutum ya shige ta, sannan zai san ta.
KASHE-KASHEN SOYAYYA.
Soyayya ta kasu izuwa gida uku kamar haka:
1 Soyayya Don Sha’awa.
2 Soyayya Don Abin Duniya.
3 Soyayya Ta Ha’ki’ka Ko Gaskiya.
1-SOYAYYA DON SHA’AWA: A wani lokaci mace kan ga namiji ko kuma namiji ya ga mace, sai d’aya daga cikinsu ya ga wani abu a jikin d’ayan har ya ja hankalinsa ya ba shi sha’awa, ya ji yana son wannan mutum saboda wannan abu. To irin wannan ba soyayya bace sha’awa ce da zarar d’aya daga ciki ya biya bu’katar tashi sai a fara neman hanyar rabuwa da juna.
2-SOYAYYA DON ABUN DUNIYA: Irin wannan soyayya Ita ce wadda ake yi don kud’i, ko dan kyau ko dan wani ‘kyale-‘kyalen duniya. Ita ma irin wannan soyayya ba ta cika nisa ba, da zarar abun da ake yin soyayyar dan shi ya gushe, sai a fara shirye-shiryen nesanta da juna.
3-SOYAYYA TA HAK’IK’A KO GASKIYA: Irin wannan soyayya ita ce wadda ake amfani da hankali da tinani wajen kafa ta. Duk soyayyar da ba a gina ta a kan sha’awa ko wani abun duniya, ko wani mugun nufi ba, to wannan soyayya ta gaskiya ce. Kuma ita ce irin soyayyar da take d’orewa wadda ba ta yankewa har abada.
MENENE SO DA KAUNA.
So da kauna, wani shauki/hali ne wanda ke kama da juna wurin tantancesa a ilimance, haka kuma a aikace .
Ka santuwar cewa ba kowa ke sanin abunda yake aikatawa ba a tsakanin mu, ko kuma, me masoyina masoyiyata ke yi man daga cikin wannan halaye. Kowannen anayinsu ne ba tare da mutum yasan me yake aikatawa ba, kasancewar baya iya tantancewa tsakanin biyun nan me suke nufi. Ko wannen su aikatasu halal ne a addinin muslumci, saidai wani yafi wani, daraja a idan shari'a kasancewar muhimmancin sa da amfaninsa tsakanin masoya. Hmm nasan wasu zasuyi mamaki akan cewar me ya hada addini da soyayya, tirqashi... To ka sani Madarar da zumur ilimin soyayya tatacce daga addinin muslunci, yake. Haka kuma duk wanda yabi tsarin soyayya a muslumci, ba shakka zai yi soyayya wacce take tatatta, kuma amintatta. Wacce babu yaurada ko ha'incin juna tsakanin masoya.
Menene Kauna?
= Kauna tamkar SO take sai daifa tafi So aminci, domin ita kauna bata canzawa, kuma ita kauna ba’a amutu akanta, ma’ana ba’acewa lallai sai an auri wanda ake Kauna ko sai an kasance tare dashi, in hakan bata yuwuba za’ai tashin hankali, ko a fara zargin shi abin kaunar, ita kauna ba haka takeba, ko anyi nasarar samun abin kaunar ko ba’ayiba, ana cigaba da masa fatan alheri kamar yadda kake masa a baya. Kuma ita kauna bata kwaranyewa, rashin haduwa tsawan zamani bai kwaranyar da ita.
Galibi abinda ke kawo kauna dabi’une, wato halaiyan abin kaunar suke janyo zuciya zuwa ga kaunarshi.Labels: Soyayya