ILLOLIN SHAFE_SHAFEN BILICIN


Shafe-shafe yana da illoli masu tarin yawa musamman ga ’ya mace. Na farko yakan canja wa mace launin fatarta. Fatar da ba a yi wa shafe-shafe,itatake ba da kariya daga cututtuka da sauran kwayoyin da suke yi wa fata barazana.

Fata ta asali na ba mace garkuwa daga zafin rana. Bayan mace ta yi bilicin za ta kasance cikin yawan laulayi, ba za iya yawo a rana ba domin za ta ji kamar ana kwaraya mata ruwan zafi, saboda ta rasa fatarta ta asali da ke ba ta garkuwa daga zafin rana.
Abu na biyu shi ne, mai bilicin ba za ta samu kariya daga cutar daji (kansa) ba, wadda cuta ce mai ban tsoro da wuyar sha’ani, ba kasafai aka fiye samun maganinta ba, cuta ce wadda take kama sassan jikin mutum, yawanci akan yanke gabobi ko wuraren da ta kama.
Duk wannan ya samo asali ne a sakamakon bilicin. Mai bilicin za ta rasa kuzari. Idan kafin ta fara bilicin tana iya yin aiki na tsawon sa’a uku ba ta gaji ba, to yanzu ba lallai ba ne ta iya na sa’o’i biyu ba, hakan ya haifar mata da nakasu, maimakon a nemo kiba sai aka iske rama.
Ba a nan kadai illar shafe-shafe ta tsaya ba, akwai illoli masu tarin yawa da kuma tsoratarwa. Misali bilicin na jawo gyambon ciki abin da aka fi sani da olsa (ulcer) wanda mafi yawanci akan dauketa a matsayin rashin cin abinci ke kawota.
Daga ciki akwai kassara dukkan wasu sassan jikinki masu amfani walau wadanda ake gani a zahirance da kuma wadanda ba mu iya gani, kamar irinsu: hanta da kuma koda, wadannan duk suna tagayyara ne sakamakon illar bilicin.

Labels: