HAKIKANIN ZANCE AKAN RAYUWA

Yi murmushi idan ka ga mai son ka, zai ji dadi.
 Yi murmushi idan ka ga mai kin ka, zai ji tsoro.
Yi murmushi idan ka ga wanda ya bar ka, zai yi da-na-
sani.
Yi murmushi ga wanda ka sani da wanda ba kasani ba. Murmushi karfi ne ga namiji, kwarjini ne gafuskar macce.
Makaho idan idonsa ya bude karya sandarsa yakeyi. Haka dan Adam yake da saurin manta alheri dakin tuna baya. Duk wanda za ka taimake shi yi ma sa
don Allah. Idan kana jiran godiya da sakayya dagamutane babu shakka za ka sha mamaki.



Wawa shi ke fadin abin da zai aikata, mai kuri
shi ke bayyana abinda ya aikata. mai natsuwa aikinsa
ne ke bayyana matsayinsa.
Gishiri da Sugar kalarsu daya ce. Banbancinsu
yana bayyana ne idan aka dandana. Haka mutane su
ke, sai an gwada akan san na kwarai.
Har abada akwai zukatan da ke son ka ko dakana munana ma su. Akwai kuma ma su kin ka duk
yadda ka kyautata ma su. Kowa da kiwon da ya karbeshi
Idan namiji bai ji dadin aure ba zai yi tunanin
kara mata don ya samu jin dadi. Idan kuma ya ji
dadi zai yi tunanin karawa don ya kara jin dadi.
Mata ku yi hakuri karin aure dabi'a ce a cikin
mazajenku.
Marar gaskiya kamar mai yagaggen wando ne duk
inda zai zauna sai ya rinka kame-kame. Mai gaskiya
a natse yake zamansa.

Labels: