Malam Adamu Ciroma ya rasu yana da shekaru 84 a
duniya a asibitin Nizamiye dake abuja ranar
alhamis.
Jiga-jigan yan siyasar nijeriya da masu rike da
muhinmman mukamai a fadin kasar sunyi
jimamin mutuwar tsohon gwamnan babban
bankin Nijeriya, Adamu Ciroma.
Malam Adamu Ciroma ya rasu ranar alhamis 5 ga
watan Yuli » a asibitin Turkish Nizamiye dake nan
garin Abuja bayan rashin lafiya da ya fama da ita.
Shugaban kasa da sauran yan siyasa sunyi jimamin
mutuwar sa
Shugaba Muhammadu Buhari a cikin wata sakon
ta'aziya da ya fitar, shugaban yace kasar baza ta
manta da irin gudumawar da tsohon ministan yayi ba.
Shugaban yace kasar zata karrama shi bisa taimakon
da yayi wajen gina dimokrdaiya a kasar kuma
tarihin sa zai zama abun koyi ga sauran yan siyasa
dake da manufar yi ma al'umma hidima.
Daga karshe yayi ma marigayin addu'a tare da baiwa
iyalen da ya bari fatan samun hakurin jure rashin
da suka samu.
Shima shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, a
wata sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter ya
kira marigayin a matsayin wanda yayi kasa hidima
mara iyaka. Yace mutuwar sa babban rashi ne ga
Nijeriya.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar,
yace daga cikin abubuwan da suka taimake shi a
rayuwa shine tunatarwa da shawarwari da ya samu
daga marigayin sanda yake da rai.
Atiku yace tsohon ministan ya bar tarihi a harkar
siyasa da shugabanci.
Anyi sallar jana'izar marigayi a Abuja
Anyi jana'izar shi a nan masallacin birnin tarayya
yammacin ranar alhamis » . Manyan masu hanu da
shuni a harkar siyasa sun halarci jana'izar sa cikin
su akwa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki
da gwamnan jihar Yobe da Kebbi tare da Sarkin garin
Fika dake jihar Yobe.
Shima shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa,
Alhaji Abba Kyari ya halarci jana'izar marigayin.
Malam Adamu Ciroma shine gwamnan bankin
tarayya tsakanin watan Satumba na 1975 zuwa Yuni
na 1977.
Haifafen dan jihar Yobe ya rike matsayin ministan
Kudi da ministan noma a karkashin mulkin tsohon
shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Bayan haka ya
kuma rike mukamin ministan noma.
Yana daya daga cikin kashin bayan da suka gina
jam'iyar PDP kuma shine shugaban yakin neman
zaben Obasanjo gabanin zaben 2003.
Mutuwar sa ya girgaza zukata da dama duba da
gudunmawar da ya bayar wajen harkokin siyasa da
kuma raya kasar.
Labels: Kimiyya da fasaha