Hukumar 'yan sandan jihar Borno ta bayyana cewa, kimanin mutane 13 ne suka rasa rayukan su a wani harin kunar bakin wake na ranar Asabar da ya afku a kasuwar garin Biu ta karamar hukumar Biu dake jihar ta Borno.
Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, Victor Isuku, shine ya tabattar da afkuwar harin a wata ganawa da manema labarai a birnin Maiduguri.
Mista Isuku ya bayyana cewa, adadin mutane 53 ne suka raunata yayin da 'yan mata biyu suka tayar da bama-bamai daure a jikin su.
Rayuka 13 sun salwanta, 53 sun raunata a wani sabon harin kunar bakin wake na Boko Haram a garin Biu
Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa, wannan lamari ya afku ne da misalin karfe 11:40 na ranar Asabar, inda wasu 'yan mata biyu suka sakuda kansu cikin kasuwar sanye da bama-bamai a jikin su kuma suka tayar da kawunan su.
Hausansi ta ruwaito da sanadin jaridar Premium Times cewa, tuni an riga da killace gawarwakin wadanda suka riga mu gidan gaskiya, yayin da aka mika wadanda suka raunata zuwa babban asibiti na garin Biu.
Labels: Kimiyya da fasaha