Sanata Wamako ya tallafa wa wani makarantar Islama a Sakkwato da naira miliyan 1.4
- Daliban makarantar wadanda suka kammala karatu su 80 sun sami kyautar naira 400,000
- Sanatan ya kuma ba da naira miliyan 1 ga makarantar don inganta ayyukan ta
Sanata mai wakiltar jihar Sakkwato ta arewa a majalisar dattijai, Aliyu Wamakko ya ba da kyautar naira miliyan 1.4 ga wata makarantar Islama ‘Yushau Abdullahi Nizzamiya Islamiya’ wanda ke Arkilla a Sakkwato don taimakawa ayyukan ta.
Sanarwar ta ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba wanda mataimaki na musamman ga sanatan, Alhaji Bashir Mani ya bayar, ya bayyana cewa, 'yan makarantar wadanda suka kammala karatu su 80 sun sami kyautar naira 400,000.
Ya kara da cewa sanatan ya kuma ba da naira miliyan 1 ga makarantar don inganta ayyukan da ake gudanarwa da kuma kayan aiki.
Sanata mai wakiltar jihar Sakkwato ta arewa a majalisar dattijai, Aliyu Wamakko
Hausansi ta tattaro cewa, Mani ya ce, sanata, wanda shi ne kuma shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan Ilimi na sakandare, ya bukaci 'yan Najeriya masu arziki su tallafawa kokarin gwamnati a fannin ilimi a duk matakai.
Ya ce, "Ya kamata a kara zuba jarurruka a harkokin ilimi kuma a kara kafa makarantun masu zaman kansu”.
"Saboda haka, ina yaba wa mai wannan makarantar don tabbatar da kafuwar ta da kuma ci gaba da daukar nauyin ayyukan ta".
Ya ce sanata Wamakko ya bukaci masu hannu da suni suyi koyi da mai makarantar, Alhaji Yushau Abdullahi don mayar da darajar ilimi.
Labels: Kimiyya da fasaha