Rikicin Kudus: Watakila Najeriya ta samu kan ta cikin matsala saboda marawa Amurka baya 

Tun bayan da ya ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Israila, Donald Trump na shan suka da caccaka, daga kasashen duniya, ciki har da Najeria
Amurka na iya dakatar da gudumuwar da ta ke ba Najeriya
Gwamnatin Amurka, ya zuwa yanzu, bata dakatar da taimako da take aikowakasashe ba, ciki harda Najeriya, duk da alkawarin da ta dauka na yin hakan muddin kasashen suka ki mara mata baya a majalisar dinkin barakar duniya.
A cewar shugaban na Amurka dai, bazai kara biyan kudin taimako da a baya kasar tasa ke mikawa matalautan kasashe ba, wanda ake kira USAID, muddin suka kushe kasar tasa, kumma sai suka kushe din.
Watakil dai a kasafin kudinsa na badi, shugaba Trump din ya iyar da nufinsa na kin bayar da gudummawar da yake bayarwa ga kasashen, domin dai, ansan shi da riko.

Labels: , , , ,