- Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP na zawarcin Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga APC
- Bayanai sun nuna cewa manyan jam'iyyar PDP sun fi amince a kan tsayar da Kwankwaso mai makon Atiku
- Jigon ‘yan siyasar suna ganin koda APC ta tsaida shugaba Buhari a 2019 Kwankwaso ne kadai zai iya ja da shi
Rahotanni sun bayyana cewa wasu jiga-jigan babban jam’iyyar adawa ta PDP na ci gaba da matsawa tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabi'u Musa Kwankwaso lamba kan ya bi sahun Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar APC.
Bayanai sun tabbatar cewa wannan ne ma yasa a kwanakin baya Kwankwaso ya gana da shugaban PDP, sanata Ahmed Makarfi da Abdul Ningi a Kaduna a inda suka tattauna batun makomar siyasarsa.
Kawo yanzu dai bayanai sun nuna cewa manyan jam'iyyar sun fi amince a kan tsayar da Kwankwaso a matsayin dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar PDP ganin yadda ya karbu a kowane sashin kasar nan fiye da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Suna kuma ganin shine koda jam'iyyar APC ta tsaida shugaba Buhari a 2019 Kwankwaso ne kadai dan takarar da zai iya ja da shi a 2019 musamman idan akayi la'akari da zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da aka yi a shekara ta 2015 inda Kwankwso ya zo na biyu a zaben.
Majiyar Hausansi ta ruwaito cewa wadanda suke bukatar Kwankwaso ya sauya sheka zuwa PDP su ne tsohon mai magana da yawun jam'iyyar PDP ta kasa, Bar. Abdullahi Jalo da shugaban amintattu na jam'iyyar, sanata Walid Jibrin da kuma shugaban magoya bayan Kwankwaso, Alhaji Sharu Garba Gwammaja.
Jalo ya bayyana cewa ya yi fatan ganin tsohon gwamnan jihar Kano ya canza sheka zuwa jam’iyyar PDP. A yayin da magoya bayan tsohon gwamnan ke ganin gwara jigon dan siyasar ya koma PDP domin APC ba zata bashi damar kaiwa ga cimma manufofin siyarsar sa ba.
Labels: Kimiyya da fasaha