Shahararriyar kasuwar Pantekan dake unguwar Tudun wada na jihar Kaduna, ta kama da wuta a tsakar daren Juma’a da misalin karfe 12 na dare, kamar yadda NAIJ ta ruwaito.
Rahotanni sun nuna an samu gagarumar asara ta dukiya, wanda ka iya kaiwa na daruruwan miliyoyin Nairori, sakamakon kasuwar ta kunshi yan kasuwa daban daban, amma ba’a samu rahoton asarar rayuka ba.
Gobara
Wannan kasuwa ta yi suna wajen siyar da katako, karafa, da sauyan kayayyakin gine gine, kuma tana kallon kwalejin kimiyya da fasaha na jihar Kaduna, sa’annan tana gab da gidan gwamnatin jihar Kaduna.
Gobarar
Har sai da misalin karfe 5 na Asuba sa’annan aka samu motar yan kwana kwana tazo don kokarin kashe wutar dake ci bal bal, yan kwana kwanan sun yi iya kokarinsu, amma abin ya fi karfinsu, don ko a lokacin da suka zo, wutar ta riga ta ci sosai.
Da faruwar abin, Sanata Shehu Sani ya bayyana jajensa ga jama'a da suka yi wannan rashi, "Ina Ma Jama'an Kasuwar Panteka Jaje bisa ga tashin gobaran da ya afka masu.Allah ya tsayar nan.Allah yasa kaffara ne.Allah ya maida dubun abin da aka rasa.Amin."
Gobara
Da fatan Allah ya baiwa wadanda abin ya shafa juriyar rashi, ya mayar musu da arzikin da yafi alheri, Ya kuma kiyaye gaba.
Gobara
Labels: Kimiyya da fasaha