Mai gayya mai aiki: Kwankwaso ya shilla ƙasar Masar don ceto ɗaliban jihar Kano 37 da gwamnati tayi watsi dasu (Hotuna)

A yanzu haka, tsohon gwamnan jihar Kano, kuma sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na can kasar Masar, inda ya tafi don taimaka ma daliban jihar Kano dake karatu a kasar.

Hausansi ta samu wannan rahoto ne cikin wata hira da gwamnan yayi da gidan rediyon Dala FM, dake jihar Kano, inda ya bayyana musu manufarsa ta zuwa kasar Masar.

Kwankwaso ya tafi kasar Masar ne da nufin taimaka ma daliban jihar su 37 dake karatu a jami’ar Al-Mansoura, inda suke karantar kiwon lafiya, fannin aikin Nas, wanda ake zargin gwamnatin jihar tay watsi dasu.

Kwankwaso Masar

Rahotanni sun bayyana cewar dama gwamnatin jihar Kano, karkashin tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ne ta tura daliban karatu zuwa jami’ar Al-Mansoura.

Kwankwaso a jami'ar

Kafin wannan zuwa da Sanata Kwankwaso yayi, daliban sun shiga mawuyacin hali, sakamakon rashin biya kudin makarantansu, wanda hakan ke barazana ga karatunsu a jami’ar.

Labels: