Ko ka san mutane nawa 'Yan Boko Haram su ka kashe a mulkin Buhari?

Boko Haram sun kashe sama sa mutane 1,000 a shekaru 2

- Haka kuma an kashe 'Yan ta'adda fiye da 600 a wannan lokaci

- Amma har wa yau ana samun kisan bakin wake a wasu wurare

Wani bincike da Jaridar Daily Trust tayi kwanan nan ya nuna cewa 'Yan Boko Haram sun kashe fiye da mutane 1,000 daga 2015 zuwa karshen 2015.

Har yanzu Boko Haram na barna a Gwamnatin Buhari

Daga karshen shekarar 2015 zuwa yanzu watau shekaru 2 dai an rasa mutane 1,088 ta sanadiyyar 'Yan ta'addan Boko Haram. Mutanen da su ka rasu a bara ma dai ba su kai wadanda aka kashe a banan nan ba. A bana kurum an kashe mutane sama da 700.

Haka kuma an yi nasarar kashe 'yan ta'adda sama da 600. Mafi yawan 'Yan Boko Haram din sun rasa ran su ne a bara don kuwa bana abin ya canza. 'Yan Boko Haram yanzu sun rage fito-na-fito da Sojojin kasar sai dai su labe. An dai samu sauki kwarai bayan hawan Shugaban Kasa Buhari mulki.

'Yan Boko Haram na cigaba da yi wa Bayin Allah kisan mummuke da na bakin wake duk da Gwanabtin Tarayya tace an ci karfin 'Yan Boko Haram a Kasar tuni. Shugaban Hafsun Sojin kasar Laftana Janar Tukur Buratai yayi kokarin kana Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau amma ya gaza.

Labels: