- Tsohon shugaban kasa Jonathan ya maida martani kan zargin da gwamna Shettima yayi a kansa lokacin taron kaddamar da wata littafi game da mulkin Jonathan a Abuja
- Jonathan yace littafin da tsohon ministan matasa da cigaban wasanni ya wallafa tana cike ne da karereyi da kuma gulma ne kawai
- Jonathan ya zargi gwamna Shettima da hannu cikin sace 'yan matan Chibok da kuma yin zagon kasa ga yunkurin gwamnatin tarayya na magance ta'addanci a Jihar
Tsohon shugaba Goodluck Jonathan siffanta littafin da tsohon Ministan Matasa da Cigaban wasanni, Mallam Bolaji Abdullahi a matsayin tarin gulma da karerayi
Littafin da aka kaddamar a ranar Alhamis a garin Abuja tayi fashin baki ne kan yadda tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya samu mulkin Najeriya cikin sauki, da kuma yadda mulkin kasar ta sullube daga hannun sa.
Tsohon shugaban kasa Jonathan ya zargi gwamnatin Jihar Borno da ruruta wutar Boko Haram
A wajen taron kaddamar da littafin, Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ya siffanta tsohon Shugaban kasa Jonathan a matsayin shugaba mara alkibla wanda ya tafka kurakurai da dama lokacin yana mulkin kasar.
Sai dai tsohon shugaban kasan ya maida marta ta bakin hadimin sa Mista Ikechukwu Eze inda yace kallaman gwamnan na cike da hassada, Ya karya dukkan zargin da gwamnan yayi inda ya bayyana irin nasarorin da gwamnatin sa ta samu.
Jonathan ya shawarci gwamnan ya fito fili ya fadawa duniya rawar da ya taka wajen sace 'yan matan Chibok, ya kuma zargin gwamnan da hannu wajen yima gwamnati zagon kasa a yakin da takeyi da Boko Haram.
Jonathan ya kallubalanci gwamnan ya fadawa al'umma abinda ya aikata da zunzurutun kudi sama da naira biliyan 60 na kananan hukumomi da Senata Ali Modu Sherrif ya bar masa.
Labels: Kimiyya da fasaha