Hukumar NNPC tayi magana game da yiwuwar karin kudin man feturĀ 

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake kula da harkokin kamfunnan mai na kasa watau Nigerian National Petroleum Corporation, NNPC a turance ta bayyana cewa babu maganar karin kudin mai daga hukumar kamar yadda ake ta yayatawa a cikin kasar nan.

Haka kuma hukumar ta NNPC ta bayyana cewa jama'ar kasa su kwantar da hankalin su don kuwa hukumar na da isasshen mai a ajiye cikin rumbunan su da zai ishi 'yan kasar har zuwa sabuwar shekara mai kamawa.

Hukumar NNPC tayi magana game da yiwuwar karin kudin man fetur

Hausansi dai ta samu cewa hukumar tayi wannan jawabin ne jim kadan bayan da kungiyar nan ta masu harkallar man ta kasa watau Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria, IPMAN ta sanar da cewar ta janye harkokin ta daga jihar Legas.

A wani labari kuma, Gwamnan Babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria, CBN, a turance Mista Godwin Emefiele ya bayyana cewa yanzu haka kudin da ke a cikin baitulmalin kasa ya kai Dalar Amurka biliyan 35.2 daga Dala biliyan 23 a watan Oktobar shekarar da ta gabata.

Labels: