Hausansi Hausansi ta kawo muku jerin hotunan shahararrun 'yan kwallon kafa da ba zasu taka leda ba a gasar kwallon kafa ta kofin duniya da za a kara a shekarar 2018.
Wannan gasa dake zuwa duk bayan shekaru 4, tana samun daukar hankalin duniya sakamakon nishadantar wa da kuma fitattun 'yan kwallo dake kara a lokaci guda da junann su, domin yiwa kasashen su hidima da bajinta.
Gasar da za a kara a kasar Rasha a tsakanin kasashe 32 da suka samu cancantar fitowa daga cikin jerin kasashe na nahiyyar su, inda wasu kasashen ba suyi nasarar samun cancanta ba, wanda hakan ya sanya gasar zata zama abin kallon ko kin labari ga wasu manyan 'yan kwallo.
Ga jerin hotuna tare da kungiyar kwallon kafa ta 'yan kwallo da ba zasu halarci ba, da kuma kasashen da suke taka wa leda.
1. Gareth Bale, na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid. Ba zai halarci gasar ba sakamakon rashin cancantar kasar sa ta Wales.
Gareth Bale
2. Alexis Sanchez: Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kuma dan kasar Chile.
Alexis Sanchez
3. Riyad Mahrez : Kasar Algeria - Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City
Riyad Mahrez
4. Arjen Robben: Kasar Holland - Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich
Arjen Robben
5. Arturo Vidal: Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich - Kasar Chile
Arturo Vidal
6. Pierre-Emerick Aubameyang:Kasar Gabon - Kungiyar kwallon kafa ta Borrusia Dortmund
Pierre-Emerick Aubameyang
7. Jan Oblak: Mai tsaron raga na kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, kuma dan kasar Slovenia.
Jan Oblak
8. Edin Dzeko: Na kasar Bosnia-Herzengovina - Kungiyar kwallon kafa ta A.S Roma
Edin Dzeko
9. Leonardo Bonucci: Kasar Italiya - Kungiyar kwallon kafa ta A.C Milan
Leonardo Bonucci
10. Zlatan Ibrahimovic: Sakamakon daina buga wa kasar sa ta Sweden kwallon kafa, dan wasan na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ba zai taka leda a gasar kofin duniya ba.
Zlatan Ibrahimovic
Labels: Kimiyya da fasaha