Dandalin Kannywood: Ainahin tsakani na da Rahma Sadau - Inji Jaruma Nafisa Abdullahi

A wani karon kuma, jaruma Nafisa Abdullahi ta fito tayi bayani dalla-dalla game da ainihin alakar ta da jaruma Rahma Sadau musamman ma a farfajiyar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood duba da yanayin yadda ake yayata cewa dangantaka a tsakanin su tayi tsami.

Jarumar dai tayi wannan karin haske ne yayin wata fira da Weekly Trust jim-kadan bayan ta amshi kyautar ta ta gwarzuwar jaruma a fina-finan Afirika a birnin Landan a kwanan baya inda ta bayyana cewa ita zaune take lafiya da kowane abokin sana'ar ta.

Dandalin Kannywood: Ainahin tsakani na da Rahma Sadau - Inji Jaruma Nafisa Abdullahi

Hausansi dai ta samu cewar da aka tambaye ta ko da gaske ne ba su ga-maciji da junan su ita da korarrar jarumar nan Rahama Sadau, sai ta kada baki tace ita dai gaskiya wannan zargin ba gaskiya bane don kuwa babu wani tsabani a tsakanin su yanzu.

Jarumar ta kuma bayyana cewa ita Rahma Sadau kanwa ce a wurin ta sannan kuma dukkan su suna yin aiki ne a karkashin kamfani daya don haka ba gaskiya bane ace kuma suna fada da junan su.

Labels: