Darakta Janar na masu tsaron fadar shugaban kasa, Lawal Daura, ya bayyana cewa shine ya sahawarci ministan shari’a Abubakar Malami da ya hadu da Maina a kasar waje
- Ya bayyana cewa Malami ya fada mashi batun bukatar Maina na son ganawa da shi, amma cewa ya shawarci Malami da ya hadu da tsohon shugaban fansho din a gaban shaida na uku
- Daura ya ci gaba da cewa ya amince da ba Maina kariya ne saboda hukumar SSS ta samu bayanin cewa rayuwarsa na cikin hatsari
Lawal Daura, Darakta janar na hukumar SSS, ya bayyana cewa shine ya ba ministan sharia Abubakar Malami shawarar haduwa da tsohon shugaban hukumar fansho a kasar waje, jaridar Premium Times ta rahoto.
Daura ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gabata a gaban kwamitin majalisar wakilai dake binciken al’amarin dawo da Maina ma’aikatar tarayya.
Hausansi ta tattaro cewa shugaban na hukumar SSS ya bayyana cewa ya shawarci Malami da ya hadu da Maina a gaban shaida na uku.
Ni na shawarci Malami da ya hadu da Maina a kasar waje – Shugaban SSS Daura
Daura ya ci gaba da bayyana dalilin da yasa ya ba tsohon shugaban fansho din kariyar tsaro.
Labels: Kimiyya da fasaha