Dalilin da yasa bai kamata Buhari yayi zancen dawowa na biyu ba a yanzu – Sage Africa - 

Kungiyar Sage Africa ta ce lallai shugaban kasa Muhammadu Buhari bai cika alkawaran zaben da ya dauka ba balle har ya bashi damar sake komawa mulki a karo na biyu

- Kungiyar tayi ikirarin cewa manufofin gwamnatin Buhari ya haifar da rashin aikin yi

- Sun kara da cewa shirin Buhari na sake takara cin fuska ne ga yan Najeriya

Duk da ci gaba da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi a shakaru biyu da watanni da suka shige, kungiyar Sage Afrika, ta kaddamar da cewa shugaban kasar bai cancanci dawowa shugabanci karo na biyu ba

A cewar kungiyar, shugaba Buhari bai gama cika alkawaran zabe da ya dauka ba.

A lokacin kawo wannan rahoto, fadar shugaban kasa bata rigada ta maida martani ga zargin kungiyar Sage Africa ba.

Jaridar Punch ta rahoto cewa kungiyar sun shawarci Buhari da ya guji kudirin sake tsayawa takara a irin wannan lokaci da al’umman kasar ke cikin garari a karkashin gwamnatin.

Rahoton ya kawo cewa daraktan kungiyar Joshua Asubiojo, da yake magana a ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba, a Abuja inda yayi ikirarin cewa ayyuka da manufofin wannan gwamnati ya dada tabarbare al’amarin rashin aikin yi a kasar.

Labels: