Bikin Maulidi: An sake gamo tsakanin kungiyar Shi'a da jami'an 'yan sanda a jihar Kaduna

A ranar Jumma'ar da ta gabata ne tarnaki ya tashi a birnin jihar Kaduna, yayin da mambobi na kungiyar IMN (Islamic Movement Of Nigeria) wato kungiyar Shi'a suka sake arangama da jami'an 'yan sanda a yayin gudanar da bikin maulidi na kungiyar domin tuna wa da ranar haihuwa ta fiyyayen halitta.

A yayin gudanar da tattaki tare da yin wake na daruruwan mambobin shi'a akan manyan hanyoyin jihar ta Kaduna, jami'an 'yan sanda sun yi gaggawar tarwatsa wannan gangami da jefa musu barkonon tsohuwa da kuma harbe-harbe na harsashai a saman iska

Jami'an na 'yan sanda sunyi kokarin kwantar da tarzoma da samar da kwanciyar hankulla yayin da wasu masu tayar da kayar baya suka yi yinkurin ta'azzarar da lamarin a jihar.

Mataimakin kakakin kungiyar ta IMN, Mallam Abdulmumini Giwa, yayi tir da wannan hari na jami'an 'yan sanda a wata ganawa da manema labarai inda ya bayyana cewa, "A yau 12 ga watan Rabiu Awwal, wanda yayi daidai da ranar haihuwar fiyyayen halitta kuma muna murna da wannan rana a matsayin mu na al'umma ta musulmi. Ba mu da masaniya ta dalilin da yasa jami'an 'yan sandan suka kawo mana farmaki."

Kungiyar Shi'a

"Kamar yadda aka saba, musulmai sukan gudanar da biki na murnar ranar haihuwar fiyyayen halitta a baki daya duniya, saboda haka kungiyar IMN ta fito domin itama ta bayyana farin cikin ta da wannan rana kamar yadda sauran musulmai suke ci gaba da gudanarwa tun gabatowar wannan wata."

Ya ci gaba da cewa, "wannan yinkuri na jami'an 'yan sanda yana aika sakon mai rauni ga al'ummar jihar kaduna baki daya da cewar babu wani romon demokuradiya da yayi saura. Watakila gwamnati ba dakile kungiyar IMN kadai take yi ba, face gaba daya al'ummar musulmi dake bikin murna ta ranar haihuwar fiyyayen halitta."

"Sun shiga wata riga ce domin yakar musulunci da musulmai, domin wannan rana ce ta farin cikin haihuwar fiyayyen halitta, ina dalilin su na kawo mana farmaki."

Ya kara da cewa, tuni kungiyar IMN ta shigar da karar shugaba kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai gaban kotun duniya ta ICC(International Criminal Court), bisa laifukan kiyashi da suka yiwa wasu mambobin mu.

Labels: