Babbar magana: Kotu za ta kira Jonathan ya bayyana a gaban ta

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan zai bayyana gaban Kotu

- Za a aikawa Goodluck Jonathan sammaci a mako mai zuwa

- Ana cigaba da shari’a da Olisah Metuh na Jam’iyyar PDP

A dazun nan ne mu ka ji cewa tsohon Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan zai bayyana a gaban Kotun Tarayya yayin da ake nema ya bada shaida a wata shari’a.

An taso Jonathan gaba wajen shari'ar Metuh

Babban Kotun Tarayya da ke Abuja tace ta gagara kiran tsohon Shugaban ya bayyana a gaban ta kwanakin baya. Jaridar The Punch tace mai gadin gidan Shugaban ya bayyanawa Ma’aikatan Kotun cewa Jonathan yayi tafiya zuwa wajen kasar.

Lauyan da ke kare wanda ake zargi Barista Emeka Etiaba yace an tasa Olisha Metuh a gaban wajen ganin ya kawo Jonathan ya bada shaida a Kotu. Ana dai sa rai Jonathan zai dawo kasar a Rana 11 ga wata wanda a lokacin za a nemi ya bayyana a gaban Kuliya.

A baya dai an yi yunkurin ganin tsohon Shugaban Kasar ya bada shaida a gaban Kotu amma abin ya faskara. Lauyan da ke karar tsohon Jami’in Jam’iyyar PDP yace dole wannan karo a samu Goodluck Jonathan ya hallara a gaban shari’a.

Labels: