Hadimar shugaban kasa na musamman a shafukan zumunta, Lauretta Onochie, tace mai yiwuwa Atiku Abubakar ya rasa makomar siyasar sa
- Hadimar shugaban kasar ta bayyana cewa Buhari baya gasa da tsohon mataimakin shugaban kasar a halin yanzu
Fadar shugaban kasa ta bayyana kudirin Atiku Abubakar na cewa zai kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a wani zabe a matsayin alamu dake nuna cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi hannun riga da gaskiya.
Hadimar shugaban kasa na musamman a shafukan zumunta, Lauretta Onochie ce ta sanar da hakan yayinda take magana a shirin gidan talbijin din Channels Television, Vanguard ta ruwaito.
Lauretta Onochie ta maida martini ga ikirarin Atiku na cewa gwamnatin Buhari ta gaza
Onochie ta bayyana cewa koda a karamar hukuma na jihar Adamawa Atiku ba zai taba yin nasarar zabe ba, inda tace ya rigada yayi hannun riga da gaskiya.
Onochie ta kuma yi watsi da ikirarin Atiku na cewa gwamnatin Buhari ta gaza isar da alkawaran zabe da ta dauka.
Ta ce jam’iyyar PDP ta durkusar da Najeriya tsawon shekaru 16 kuma sannan cewa a karkashinta ne tattalin arzikin Najeriya ta durkushe.
Labels: Kimiyya da fasaha