Arewa bata tsayar da Buhari kadai a matsayin dan takarar shugabancin kasa a 2019 ba – Kungiyar matasan Arewa 

Shugaban kungiyar matasan arewa ya kalubalanci furucin shugaban kungiyar dattawan arewa, Paul Unongo, kan tsayar da shugaban kasa Buhari a matsayin dan takarar shugabancin kasa a 2019

- Shugaban kungiyar ta AYCF, Alhaji Shettima Yerima, ya jaddada cewa shugabancin kasa na yankin arewa ne har sai 2023 don haka ya rage garesu su cike gurbin da wani

Kungiyar matasan Arewa ta yi watsi da jawabi daga shugaban kungiyar dattawan Arewa, Paul Unongo, dake cewa yankin arewa sun tsayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar shugabancin kasa a 2019.

Alhaji Shettima Yerima, shugaban kungiyar matasan arewan, a wani jawabi da aika ga hausansi a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, yace Paul Unongo na yi wa kansa magana ne kamar kullun ba wai ga kungiyar dattawan arewa ko arewa baki daya ba.

Ba buhari kadai bane dan takarar arewa a zaben 2019 – Shettima Yerima

Shugaban kungiyar ta AYCF yace Unongo baida ikon da zaiyi wa arewa magana akan ko wani al’amari saboda maganasa bai tafi daidai ba.

Shugaban kungiyar matasan arewan ya jaddada cewa shugabancin kasa na yankin arewa ne har sai 2023 don haka ya rage garesu su cike gurbin da wani.

Labels: