Wasu 'yan bindiga dadi da ake kyautata zaton fulani makiyaya ne da sanyin safiyar jiya suka farwa wasu kauyuka biyu da suka hada da Lawuri da a cikin karamar hukumar Demsa ta jihar Adamawa suka kuma kone su kurmus kamar dai yadda wani ganau ya shaidawa majiyar mu.
Karamar hukumar ta Demsa dai tana shan fama da sabbin hare-hare tun bayan da rikicin kabilanci ya faru a karamar hukumar Numan dake makwaftaka da ita a cikin satin da ya gabata duk kuwa da jami'an tsaron da aka jibge.
Yadda 'yan bindiga suka kone kauyuka 2 kurmus a jihar Adamawa - Inji wani ganau
Hausansi dai ta samu cewa daya daga cikin mutanen kauyukan da lamarin ya auku ya bayyanawa majiyar mu cewa: "Tabbas maharan sun zo inda muke suka kuma fatattake mu daga gidajen mu tare da kone gidajen kurmus."
A dayan bangaren kuma mun samu cewa gwamnatin ta jihar Adamawa tuni ta bayyana bacin ranta tare da jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su sannan kuma ta sha alwashin karo jami'an tsaro da zummar tabbatar da zaman lafiya.
Labels: Kimiyya da fasaha