Zamu maida Koriya ta Arewa toka idan fada ya tashi - Inji Kasar Amurka

Kasar Amurka karkashin jagorancin shugaban ta Donald Trump ta sha alwashin mayar da kasar Koriya ta Arewa toka idan dai har ta kuskura ta cigaba da takalar ta fada yayin da kuma ta roki dukkan sauran kashashen duniya da su yanke alakar su ta difulomasiya da su.

Kasar ta Amurka dai ta bayyana hakan ne a yayin wani taron gaggawa da ta kira na jami'an tsaron ta da nufin tattauna batun barazanar da kasar ta Koriya ta Arewa ta yi mata na yiwuwar harba mata makamin kare dangi.

Zamu maida Koriya ta Arewa toka idan fada ya tashi - Inji Kasar Amurka

Hausansi ta samu daga bakin Ambasadan kasar Amurka din a kasar Koriya ta Arewa mai suna Nikki Haley ya shaidawa majalisar tsaron cewar: "Shugaban kasar Koriya ta Arewa a jiya kam tabbas yayi ikirarin da idan ba'ayi hankali ba zai iya jaza yaki a tsakanin mu."

Daga nan ne kuma sai ya bayyana cewa to tabbas lallai ba shakka idan har hakan ta faru to kasar ta Amurka ba zata yi kasa a gwiwa ba har sai ta mayar da abokiyar karawar tata toka ta bace daga doron kasa.

Labels: