Zaben gwaji: Atiku ya kada Buhari, Jonathan da Kwankwaso da gagarumin rinjaye

Labarin da muke samu daga majiyar mu na nuni da cewa fitaccen dan siyasar nan kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya kada shugaba Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan da kuma Sanata Kwankwaso a wani zaben gwaji da aka gudanar a dandalin Tuwita.

Wani dandalin siyasa ne ne dai mai suna Micro Blogging da ke da shafi a dandalin sada zumuntar na Tuwita ne dai ya gudanar da zaben gwajin da a halin yanzu ya jefa masoya Atiku Abubakar din cikin matukar jin dadi.

Zaben gwaji: Atiku ya kada Buhari, Jonathan da Kwankwaso da gagarumin rinjaye

Hausansi dai ta samu cewa dandalin ya tambari mabiyan sa ne ko wa za su zaba a tsakanin gaggan 'yan siyasar kasar da suka hada da shugaba Buhari, tsohon shugaba Jonathan, sai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku sai kuma a karshe suka sa Sanata kuma tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso.

Mun samu dai cewa daga karshen zaben gwajin Atiku ne yazo na farko da kaso 54 cikin dari sai Jonathan yazo na biyu da kaso 24 cikin dari, sannan kuma sai shugaba Buhari da yazo na uku da kaso 21 cikin dari sai Kwankwaso da yazo na karshe da kashi 1 kacal.

Labels: