Zaben 2019 na tsakanin shugaba Buhari da Atiku Abubakar


- Mr. Femi Falana (SAN) ya ce, yana baƙin ciki game da yiwuwar cewa zaben shekarar 2019 zai kasance tsakanin shugaba Buhari da Atiku Abubakar
- Falana ya bukaci ‘yan Najeriya su kalubalanci shugabanin akan ci gaban kasar
- Lauyan ya soke lamirin fastocin Najeriya, ya ce sun fi kowane fasto arziki a duniya
Babban lauyan nan, mai kare hakkin bil adam, Mr. Femi Falana (SAN) ya ce, yana baƙin ciki game da yiwuwar cewa 'yan Najeriya za su zabi shugaba Muhammadu Buhari ko kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a zaben shekarar 2019.
Mista Falana ya bayyana haka yayin da yake magana a wani taron tattaunawa a Legas.
Ya bukaci 'yan Najeriya su yi amfani da yanar gizo don tada al'amurra masu muhimmanci ga cin gaba da kuma makomar kasar.
Mr. Femi Falana (SAN)
Har ila yau, lauyan ya kuma caccaki gwamnan jiharsa watau gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti wanda ya bayyana shi a matsayin'Trump' na jihar.
Falana ya zargi shugabannin addinin Krista, inda ya ce, “Fastoci masu karfin arziki a duniya sun kasance daga Najeriya ne, amma duk da haka mutanenmu suna fama da talauci da kuma yunwa.

Labels: