Zaben 2019 : Abun da jam'iyyar APC da PDP ya kama ta su yi kafin zabe - Olusegun Obasanjo

- Cif Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu bai ga wani abin azo agani da gwamnati APC ta yi ba
- Raymond Aleogho Dokpesi ya kai ma Obasanjo ziyara a gidan sa dake Abeokuta a jihar Ogun
- Tsohon shugaban kasan ya shawarci jam'iyyar APC da PDP da su canza yanayin siyasar idan suna son su samu nasara a zaben 2019
Tsohon shugaban kasas Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu bai ga wani abin azo agani da gwamnati APC ta yi ba.
Da gwamantin APC da jam’iyyar adawa na PDP din duk kwashikwaraf ne.
Obasanjo ya fadi haka ne a lokacin da attajirin Danjarida shugaban gidan talabijin na AIT da Daar Communications kuma dan takaran shugaban jam’iyyar PDP na kasa Cif Raymond Aleogho Dokpesi ya kai masa ziyara a gidan sa dake Abeokuta jihar Ogun
APC da PDP duk Kame-Kame su keyi – Inji Obasanjo
Tsohon shugaban kasar ya har idan jam’iyyar dake kan mulki APC da babbar jam’iyyar Adawa na PDP suna son su samu nasara a zaben 2019 dole sai sun canza yanayin siyasar su.
” Ya kuma ja hankalin jigajigan jam’iyyar PDP da cewa Idan suna ganin hukuncin da kotun koli ta zartar shine samun lafiya a jam’iyyar PDP, to su sani hakan bai yi ko kusa da samun lafiya ba. Ita kotun koli tayi aikin ta ne kawai.
“ Amma shawo kan matsalolin jam’iyyar ya na kan mambobin ta
Ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su tabbata da sun zabi shugaban nagari a zaben jam’iyyar da ke zuwa, cewa haka ne kadai zai mafita ga matsalolin d PDP ke fuskanta.
” A lokacin da nayi mulkin kasar nan sai da nayi shugabannin jam’iyya har guda hudu , saboda haka na san dadi da rashin dadin samun shugaba nagari da wanda ba nagari ba,” Inji Obasanjo

Labels: