Kwamishinan yada labarai na jihar, Dr. Mohammed Bulama, ya fadi hakan a Dutse, jihar Jigawa, inda ya halarci wani taro da ma'aikatar sadarwa ta kasa ta shirya.
Gwamnatin jihar Borno, ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar, Dr. Mohammed Bulama, ta sanar da cewar ta kammala shirin mayar da gidan tsohon shugaban kungiyar Boko Haram da aka rushe gidan tarihi.
Kashim Shettima
Kwamishinan ya ce za su adana duk wasu kayayyakin kungiyar Boko Haram domin amfanin masu neman bayani a kan kungiyar da kuma ma su yawon bude ido.
Bayan kama Muhammed Yusuf a shekarar 2009 jami'an tsaro sun rushe gidansa dake cikin garin Maiduguri.
Bulama ya ce gidan na Muhammed Yusuf nan ne tushen kungiyar Boko Haram, a saboda haka suka yanke shawarar sake gina gidan tamkar yadda yake kafin a rusa shi.
Labels: Labarai