Wani mummunan hatsarin jirgin sama ya ci rayukan wasu manyan jami’an masarautar kasar Saudiyya, ciki har da Yarima Mansour Bin Muqrin, mataimakin gwamnan yankin Asir.
Wannan hatsari ya faru ne a ranar Lahadi 5 ga watan Nuwamba, yayin da jirgin nasu ya bace a na’urar dake lura da tafiyarsa a sararin samaniya, inda jirgi ya fado a yankin Asir, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.
Shi dai Yarima Mansour, a watan Afrilun shekarar 2017 ne aka nada shi a matsayin mataimakin gwamnan yankin Asir, Majiyar Hausansi ta ruwaito ana zaton dukkanin wadanda ke cikin jirgin sun rasa rayukansu.
A yan kwanakin nan dai, Yariman kasar Saudiyya mai jiran gado, Mohammad Bn Salman ya bada umarnin kama wasu mayan jami’an gwamnatin kasar guda 11, ciki har da yayan Sarakunan kasar, wadanda ke da hannu cikin tafka badakalar cin hanci da rashawa.
A wani labarin kuma, kasar Saudiyya ta samu nasarar kama wani makami mai linzami da aka harbor zuwa kasar daga kasar Yaman, da nufin hai mata harin ta’addanci