A ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, Ibrahim Idris, sufeto janar nay an sanda ya isa gaban kwamitin da majalisar dattawa ta shirya domin bincike kan zarge-zarge dake tsakaninsa da Sanata Isa Misau.
Sufeto janar din ya samu rakiyan lauyan sa, Alex Iziyon (SAN); da kuma Sanata Ita Enang, mai ba shugaban kasa shawara na musamman a kan al’amuran majalisar dokoki.
Don haka, daruruwan masu zanga-zanga sun cike kofar shiga majalisar dokoki don nuna hadin kai ga Idris.
Gloria Ubeji, jagorar zanga-zangar tayi ikirarin cewa gangamin hadin kan na da muhimmanci bisa sauye-sauye da dama da shugaban rundunar yan sandan ya kawo ga aikin.
Yanzu Yanzu: Daga karshe, Sufeto Janar na yan sanda ya gurfana a gaban majalisar dattawa
Yanzu Yanzu: Daga karshe, Sufeto Janar na yan sanda ya gurfana a gaban majalisar dattawa
Yanzu Yanzu: Daga karshe, Sufeto Janar na yan sanda ya gurfana a gaban majalisar dattawa
Labels: Labarai