Yanzu Yanzu: Bam ya tashi a Maiduguri

Tagwayen bam sun tashi a garin Maiduguri dake jihar Borno

‘- An tayar da bama-baman ne da safiyar ranar Talata

Rahotanni sun kawo cewa tagwayen bam sun tashi a wasu yankunan Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a safiyar yau Talata, 7 ga watan Nuwamba.

Na farkon ya tashi ne da misalin karfe 8:30 na safe yayinda na biyu ya biyo baya da karfe 8:45 na safe.

Yanzu Yanzu: Bam ya tashi a Maiduguri

Tashin bam din na zuwa ne mako daya bayan jami’an tsaro sun kama wasu yan kunar bakin wake biyu yayinda suke yunkurin shiga birnin domin tayar da bam dake daure a jikinsu.

Labels: