Yanzu Yanzu: Atiku ya sauya sheka daga APC zuwa PDP 

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya sauya sheka daga jam’iyya mai ci ta All Progressives Congress (APC) zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Ya sanar da yanke wannan hukunci a wani jawabi da saki a safiyar ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwamba.
Atiku wanda yayi shiru kan yunkurin siyasar sa na gaba, yace ya yanke wannan shawara ne bayan ya nemi zabin Allah, yan uwansa da kuma magoya bayan sa.
Ya yi korafi kan yanayin abubuwa a jam’iyya mai mulki, inda ya tuna yadda ma’asasshin jam’iyyar APC ya same shi kan ya dawo jam’iyyar.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kalubalanci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewa APC jam’iyya ce dake macewa.

Labels: