Yan majalisar wakillan na tarayyar Najeriya sun yi ta shewa tare da ihun cewa 'bama so' bama so' yayin da kakakin majalisar ya sanar masu da kudurin shugaban kasa na zuwa wurin su gabatar da kasafin kudin 2018 a ranar 7 ga watan nan mai zuwa.
To sai dai fadin hakan daga bakin Honarable Yakubu Dogara ke da wuya sai kawai yan majalisar suka dauki shewa da hayaniya mai karar gaske wanda ya saka tilas kakakin dakatawa da magana har sai da komai ya lafa.
Hausansi haka zalika ta samu cewa bayan kurar ta lafa ne dai sai Kakakin majalisar ya shaidawa abokan aikin nasa cewa bai da hurumin da zai dakatar da zuwan shugaban kasar a don haka kuwa sai dai suyi hakuri don dai dokar kundin tsarin mulki ta bashi damar yin hakan.
Ya zuwa yanzu dai ba a samu gano hakikanin musabbabin dalilin da yasa yan majalisar ke kin jinin zuwan na shugaban kasar wurin su ba.