Yaƙi da ta’addanci: Babban hafsan Sojin sama ya rant

Bababn hafsan Sojin sama, Iya Mashal Sadiqye Abubakar ya kaddamar da sabon jirgin yakin da rundunar ta samu daga cikin jiragen dake fadar shugaban kasa, wanda Muhammadu Buhari ya basu kyauta.
Samfurin Bell 412, na daya daga cikin jirage biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ma runsunar Sojin samaa shekarar nan daga cikin jiragen fadar shugaban kasa guda goma sha daya.
Hausansi ta ruwaito Sadique yace sun aika da jiragen kasar Amurka da Canada don inganta na’urar daukan hoton dake jikinsu don dacewa da aikin Soja, musamman tafiyan dare. Amma sauran aikin da aka gudanar akan jiragen a Najeriya aka yi su, wanda injiniyoyin rundunar suka yi.
Rundunar ta horar da jami’anta matuka jirgi, da sauran injinoyinta akan yadda zasu sarrafa jirgin, wanda yace za’ayi amfani da shi a bakin daga, wato yankin Arewa maso gabas, inda ake fama da matsalar ta’addanci.
Daga karshen taron rantsar da jirgin, Sadique ya hau danin jirgin, inda ta tashi da shi, tayi shawagi a sararin samaniya. Tare da wakilan babban hafsan Sojin kasa, dana ruwa.

Labels: