Wata Sabuwa: Tsagerun Neja sun sake sabunta tawayen su da gwamnatin Najeriya -

Tsagerun Neja Delta da suka kai hari kan wata cibiyar ma'aikatar man fetur a yankin na su a shekarar da ta gabata sun bayar da sanarwar cewa, sun warware alkawalin su da gwamnatin Najeriya na ajiye makaman su.
Kungiyar tsagerun ta bayar da wannan sanarwar ne a shafin ta na yanar gizo a ranar Jumma'a ta yau, inda ta bayyana cewa zata dawo da cigaba da tawayen ta a ko wane lokaci daga yanzu, da cewar gwamnatin shugaba Buhari ta nuna rashin gaskiya a sulhun da suka yi da ita tare da rashin cika alkawurran da ta daukar wa yankin na Neja Delta.
Hausansi ta ruwaito da sanadin Premium Times cewa, kungiyar ta caccaki tsohon jigonta na yankin Government Ekpemupolo, wanda ya shahara da sunan Tompolo, yayin da ta ce ya gaza nuna shugabancin sa na jagorantar wadanda ke neman cikakken 'yancin su a yankin.
Wannan sanarwar ta zo ne da sanadin kakakin kungiyar Mudoch Agbinibo inda ya bayyana cewa, hare-haren da suka kai a wasu ma'aikatun ma fetur da gas ya kawo zagon kasa a shekarar da ta gabata a wasu manyan kamfanonin man fetur na duniya irin su Shell da Chevron.
Kungiyar ta kuma bayyana sunan ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi, a matsayin daya daga cikin magoya bayan dake haddasa barna ga manufofin su.

Labels: