Wata Kungiyar Musulmai ta maidawa Kungiyar CAN martani mai zafi

Kungiyar MURIC ta Musulmai ta kuma yin kaca-kaca da CAN bayan kiran da tayi kwanaki. MURIC tace idan haka ne ita ma tana da ta cewa a lamarin kasar.
Kungiyar nan ta Musulmai mai suna MURIC ta maidawa CAN martani game da kiran da tayi kwanakin nan. MURIC tace ihun da Kiristocin na CAN ke yi bai da tushe kuma ba gaskiya bane.
Kungiyar MURIC tayi kaca-kaca da CAN
Kungiyar CAN ta dage da cewa ana kokarin musuluntar da Najeriya wanda hakan ya sa Kungiyar MURIC ta ce hayaniya ce kurum Kungiyar CAN ta Kiristocin Kasar ke yi. Shugaban Kungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya bayyana wannan.
Ita ma dai MURIC ta gindaya sharuddan ta kamar Kungiyar CAN inda ta nemi Najeriya da fice daga Kungiyoyin yammacin Duniya irin su WHO. MURIC ta kuma nemi a ba Musulmai hutu a Ranar Jumu’a kamar yadda ake ba Kiristoci.
Akintola ya soki CAN inda yace tana kira a bada filaye domin gina coci a Arewa amma kuma ana rusa Masallatai a Kudancin Kasar an kuma hana Kungiyoyin Musulmai aiki. MURIC ta nemi a daina amfani har da alamar nan ta kuros a Asibitocin Kasar.

Labels: