Mahukunta a hukumar nan dake yaki da safarar mutane da sauran munanan abubuwa ta gwamnatin tarayya ta bazama ta fara neman wata mata mai shekaru 33 a duniya mai suna Perebi Otubo da a shekarun baya aka daure ta a garin Dubai ta daular larabawa saboda laifin safarar 'yan mata daga Najeriya.
Ita dai matar a halin yanzu tana boye ne a wani boyayyen wurin da mahukuntan basu sani ba a Najeriya bayan da ta samu nasarar sulalewa daga can kasar ta larabawa ta kuma dawo gida.
Wata fitacciyar 'yar safara daga Najeriya ta tsere daga inda aka rufe ta a Dubai
Hausansi dai ta samu cewa matar mai suna Perebi Otubo wadda 'yar asalin jihar Delta ce ta dawo gida Najeriya ne a cikin watan Yulin da ya gabata inda kuma har kawowa yanzu ba'a san inda ta boye ba.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa mun ruwaito cewar Hankula sun tashi a wata unguwa da ake cewa Okigwe can cikin garin Owerri, babban birnin jihar Imo a jiya Talata bayan da wuta ta kama wani gidan sharholiya sananne mai suna Stone Castle.
Labels: Labarai