Wani Gwamnan APC ya maidawa Atiku Abubakar martani

Gwamna Aregbosola ya karyata maganar Atiku Abubakar

- Atiku yace Jam’iyyar APC ba ta bi tsarin Damukaradiyya

- Sai dai Gwamnan Osun yana da ja game da wannan magana

Za ku ji cewa Gwamnan Jihar Osun Rauf Aregbosola ya maida martani ga masu sukar Jam’iyyar APC mai mulki a kasar da cewa ana buga kama-karya a cikin Jam’iyyar.

Gwamnan Osun Aregbosola ya na da ja game da kalaman Atiku

Gwamna Ogbeni Rauf Aregbosola ya bayyana cewa sam abin da wasun ke ta fada ba gaskiya bane. Gwamnan yayi wannan jawabi ne a wajen wani taro da aka yi domin bikin murnar cikar sa shekaru 7 a kan karagar mulkin Jihar Osun.

Rauf Aregbosola yake cewa Jam’iyyar APC ba ta danniya ko kama-karya, wanda yace a dalilin haka ne ma kwanan nan ta fadi zaben Sanatan Yammacin Jihar Osun. Aregbosola bai yarda da maganar su Atiku Abubakar da ya fice daga APC ba.

Atiku Abubakar ya zargi Jam’iyyar APC da Gwamnatin da buga kama-karya da rashin bin tsarin Damukaradiyya a kasar. Gwamnan ya kara da cewa Jama’ar Osun ne za su zabi wanda zai gaje shi idan ya kammala wa’adin sa a Jihar shekara mai zuwa.

Labels: