Wani dan shekara 30 ya zakkewa budurwa har lahira a jihar Osun

Wani mutum Ahmed Matunma Wokuekun, ya gurfana a gaban kotu da laifin fyade wata budurwa Dupe Lawrence mai shekaru 13 da haihuwa, har lahira a jihar Osun.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ne, Ahmed ya gurfana a gaban kotun majistire dake birnin Osogbo, inda jami'an 'yan sanda suka bayyana cewa sun kama shi ne da laifin fyade da kuma kisan kai.

Wani dan shekara 30 ya zakkewa budurwa har lahira a jihar Osun

Jami'ar 'yar sanda mai shigar da kara a gaban kotu Olusegun Elisha, ta shaidawa kotun cewa, wanda ake zargin ya aikata laifin da misalin karfe 8:00 na safiyar ranar 17 ga watan Nuwamba a yankin Ifetedo dake kauyen Mofoworade na gundumar Osogbo.

Elisha ta ci gaba da cewa, wanna laifi ya sabawa dokar karkashin sashe na 221 da sashe na 319 na kundin tsarin dokokin jihar ta tanadar tun a shekarar 2003.

Alkaliyar kotun Habibat Basiru, ba ta karbi rokon wanda ake tuhumar, inda ta ce a jefa shi gidan kaso na Ile-Ife zuwa ranar 22 ga watan Janairu na shekarar 2018 domin ci gaba da sauraron karar.

Labels: