Wani Birgediya Janar na fuskantar sharia bisa yada jita-jitan Buhari ya mutu

- A na tuhumar wani Birgediya Janar na Hukumar Sojin Kafa, da yada jita-jitan Buhari ya rasu
- A na kuma tuhumar sa da nema karban rashawa na dala 600,000
- Birgediya Janar din mai suna Lym Hassan, zai fuskanci hukuncin Soji
Wani Birgediya Janar na Hukumar Sojin Kasa, mai suna Lym Hasaan, zai fuskanci hukuncin Soji bisa yada karya na jita-jitan cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rasu, a lokacin da ya kwanta a asibiti a birin Landan, da kuma neman cin hanci daga hannun wata kamfanin kwangila.
SaharaReporters ta samu labari daga Hedkwatan Sojin na cewan a ranar 17 ga watan Janairu, Hassan ya sanar da wani mai suna Mista Yarima Ibrahim, ta wayan tarho, cewan Buhari a rasu.
addinin musulunci a fadar gwamnati
Kuma a ranar 24 ga watan Febrairu ne Hassan ya bukaci rashawa na dala 600,000 daga hannun kamfanin kwangila na OPEMS, sakamakon wani kwangila da a ka ba kamfanin na canza mazaunin asibitin Nigeria Level 11 daga Mali, zuwa mazaunin ta na dindindin a Timbuktu.
A cewar Hedkwatan Sojin, laifukan guda 2 da Hassan ya aikata, rashin da'a ne da kuma karya dokokin Hukumar ta Soji.

Labels: